'Yan fashi sun kashe likita bayan kwana daya kacal da kammala karatu

'Yan fashi sun kashe likita bayan kwana daya kacal da kammala karatu

A wani labari mai ban tausayi da takaici da Legit.ng tayi karo da shi, wasu 'yan fashi sun halaka wani likita dan Najeriya kwana guda kacal bayan kammala karatunsa a Jami'ar Legas.

Kamar yadda wani mai amfani da shafin Facebook, Adeyeye Olorunfemi ya bayyana, ya ce an kashe likitan mai suna Dr Stephen Urueye ne a gaban Asibitin Koyarwa na Jami'ar Legas, LUTH a unguwar Idi-Araba a Legas.

A cewarsa, 'yan fashin sun kai masa hari da wuka inda suka yi masa munanan rauni da hakan ya yi sanadin rasuwarsa.

Olurunfemi ya ce wannan ba shine karo na farko da ake aikata fashi a unguwar ba. Ya ce daliban Jami'ar da ke Idi Araba sun dade suna korafi a kan yawan fashi da makami da ake yi musu amma mahukuntan jami'ar ba su dauki mataki a kai ba.

DUBA WANNAN: Kannywood: Nafisa Abdullahi ta soki Buhari a kan kashe-kashen Zamfara

"Munrasa Stephen.

"Mun rasa wannan matashin likitan da ke son ya dinga ceto rayukan al'umma.

"Ya mutu sa'o'i 24 bayan kammala karatunsa bayan shekaru takwas yana gwagwarmaya a Najeriya.

"Yan fashi suka daba masa wuka a gaban asibitin koyarwan na gwamnati, LUTH."

Wata mai amfani da shafin Twitter mai suna Dakta Kel Okoro tayi juyayin rasuwar likitan da ta ce ajinsu daya.

Ta ce ya kamata a dauki matakan hana afkuwar hakan a gaba saboda mutane su samu natsuwa a wurin ayyukansu.

Ga abinda ta rubuta a kasa:

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel