Shugabancin majalisar dattawa: Ndume ya fara tattaunawa da Goje

Shugabancin majalisar dattawa: Ndume ya fara tattaunawa da Goje

Wani rahoto daga jaridar ThisDay ya nuna cewa Sanata Danjuma Goje da Ali Ndume, sun fara tattaunawa game da kudirinsu na son zama Shugaban majalisar dattawa na gaba.

Goje, tsohon gwamnan jihar Gombe wanda a yanzu ke wakiltan yankin Gombe ta tsakiya a majalisar dattawa da Ndume wanda wakiltan Borno ta kudu, duk suna neman kujerar shugabancin majalisar.

Dukkansu su biyun sun yi watsi da batun tsayar da Shugaban masu rinjaye a majalisar, Ahmed Lawan wanda jam’iyyarsu ta All Progressives Congress (APC) tayi, sannan sun c gaba da kamfen dinsu.

A bias rahoton, sanatocin biyu sun gana a farkon wannan makn a ofishn Goje dake ginin majalsar dattawan a Abuja inda suka yanke shawarar yin aiki a matsayin tawaga daya wajen neman kujerar shuganacin majalisar.

Shugabancin majalisar dattawa: Ndume ya fara tattaunawa da Goje

Shugabancin majalisar dattawa: Ndume ya fara tattaunawa da Goje
Source: Facebook

An tattaro cewa yan majalisar biyu sun amince da tattaunawa da masu ruwa da tsaki akan kudirinsu sannan suna iya sake ganawa kafin makon ya kare.

KU KARANTA KUMA: Matasan Yobe sun bukaci zababen gwamnan jihar ya bawa bangaren noma muhimmanci

Sanata Ndume ma ya jadadda cewa har yanzu yana tseren cewa: “Ba wai ina kin mutunta jam’iyyar, amma a bari mutane su zabi shugabanninsu.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa, shugaban masu rinjaye a majalisa, Sanata Ahmad Lawan, ya gana da gwamnonin APC hudu a Abuja.

An tattaro cewa ganawar da Lawan yayi da gwamnonin ya gudana ne a daren ranar Talata a karkashin ikon gwamnan jihar Yobe, Alhaji Ibrahim Geidam, wanda a yanzu shima zababben sanata ne.

Rahoton ya nuna cewa sun yi ganawar ne domin mara wa kudrin Lawan baya a matakin kungiyar gwamnonin APC.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel