Za a yi wa mutumin da ya kashe musulmai 50 a New Zealand gwajin kwakwalwa

Za a yi wa mutumin da ya kashe musulmai 50 a New Zealand gwajin kwakwalwa

Kotu ta ba da umarnin yi wa mutumin nan da ya kai hari masallatai biyu ya kashe musulmai 50 gwajin kwakwalwa

Wata babbar kotu a kasar New Zealand ta bayar da izinin yi wa mutumin nan da ake zargi da kai hari masallatai guda biyu da ke birnin Christchurch, wanda ya yi sanadiyyar kashe mutane 50 a cikin watan Maris din da ya gabata.

Alkalin babbar kotun mai suna Cameron Mander shine ya bayyana cewa kwararrun likitoci za su gabatar da bincike akan kwakwalwar mutumin domin a tabbatar da cewar ko zai iya fuskantar shari'a ko kuma yana da tabin hankali. Kotun ta na tuhumar mutumin da laifin kashe mutane 50 ba su ji ba basu kuma gani ba, sannan kuma ta kara tuhumar shi da yunkurin hallaka wasu mutane 39.

Za a yi wa mutumin da ya kashe musulmai 50 a New Zealand gwajin kwakwalwa

Za a yi wa mutumin da ya kashe musulmai 50 a New Zealand gwajin kwakwalwa
Source: UGC

Mutumin mai suna Brenton Tarrant mai shekaru 28 dan asalin kasar Australia, ya gurfana a kotun ta fefan bidiyo daga cikin gidan yarin da ya ke a gaban 'yan uwan wadanda abin ya shafa.

A tarihi dai wannan shine hari mafi muni da aka ta ba gani a kasar ta New Zealand.

KU KARANTA: Hanyoyi guda 6 da za a bi don samawa kai sassaucin zafi a wannan lokaci

Firaministar kasar Jacinda Acdern ta yi Allah wadai da harin, sannan kuma ta kira harin a matsayin abin alhini ga 'yan kasa baki daya.

Sannan Firaministar ta dauki alkawarin haramta sayar da bindigogi masu sarrafa kansu a fadin kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel