EFCC za ta kashe miliyan N288 don sakawa injin janareto mai

EFCC za ta kashe miliyan N288 don sakawa injin janareto mai

- Hukumar EFCC za ta kashe makudan kudade wurin sanyawa injin janareto mai da kuma sayen kayan abinci

- Hukumar ta ce za ta karawa wasu daga cikin jami'anta albashi da alawus

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa (EFCC) ta bayyana cewa za ta kashe miliyan N288, a wannan shekarar wurin sakawa injin janareto mai, kudin sayen abinci, da kuma sayen jarida.

Hukumar ta bayyana cewa kudin man janareto zai kai miliyan N225, sai kuma kudin sayen abinci wanda zai kai miliyan N55, sanna kudin sayen jarida zai kai kimanin miliyan N7.87.

EFCC za ta kashe miliyan N288 don sakawa injin janareto mai
EFCC za ta kashe miliyan N288 don sakawa injin janareto mai
Source: Depositphotos

Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa mai rikon kwarya, shine ya bayyana hakan jiya Alhamis a babban birnin tarayya Abuja, a lokacin da ya ke gabatar da kasafin kudin hukumar na shekarar 2019, ga kwamitin da ta ke da alhakin hakan, inda dan majalisar wakilai na tarayya Kayode Oladele (APC, Ogun) ya ke jagoranta.

KU KARANTA: Hanyoyi guda 6 da za a bi don samawa kai sassaucin zafi a wannan lokaci

Sai dai kuma kudin da aka gabatarwa majalisar tarayya na hukumar, ya ragu da yawa, inda yake nuna miliyan N111 a matsayin kudin man injin janareto, miliyan N27 kudin abinci, da kuma miliyan N3.87 a matsayin kudin jarida.

Bayan haka kuma Magu ya nuna kudurin shi na karawa ma'aikata 970 albashi da alawus.

Hukumar EFCC dai ita ce da alhakin yaki da masu ta'annati da dukiyar kasa, musamman 'yan siyasa da masu manyan mukamai da suka samu damar kwashe dukiyar kasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel