Matasan Yobe sun bukaci zababen gwamnan jihar ya bawa bangaren noma muhimmanci

Matasan Yobe sun bukaci zababen gwamnan jihar ya bawa bangaren noma muhimmanci

Wasu matasan manoma a Damaturu sun bukaci zabeben gwamnan jihar, MaiMala Buni ya fito da tsare-tsare na inganta ayyukan noma da fadada shi domin matasan su samu damar yin noma a daminan bana.

Mai magana da yawun kungiyar, Ali Modu ne ya yi wannan rokon a hirar da ya yi da kamfanin dillancin labarai na kasa, NAN ranar Juma'a a garin Damaturu.

Ya ce matasa da dama sun son fara noma domin su rika samun abinda za su tallafawa kansu a maimakon jiran ayyukan gwamnati.

DUBA WANNAN: Kannywood: Nafisa Abdullahi ta soki Buhari a kan kashe-kashen Zamfara

Ka bawa fanin noma muhimmanci: sakon matasan Yobe ga zababen gwamna

Ka bawa fanin noma muhimmanci: sakon matasan Yobe ga zababen gwamna
Source: Getty Images

"Muna kira ga gwamnati mai shigowa ta bayar da muhimmanci ga fannin noma musamman noman rani. Akwai matasan da suka kammala makarantun gaba da sakandire da yawa kuma sun son fara noma sai dai sun bukatar tallafi da goyon baya."

"Gwamnati ta tallafa mana da iri masu kyau, takin zamani, magungunan kwari da ciyawa domin mu tsundumma cikin harkar noma gadan-gadan," inji Ali.

A cewarsa, matasa da dama suna sha'awar shirin bayar da bashin manoma na Farmer Anchor Borrowers’ scheme da zababen gwamnan ya bayyana a lokacin yakin neman zabensa.

"Zababen gwamnan ya yi alkawarin zai mayar da hankali a kan fannin noma a jihar mu kuma ya kawo tsari irin na bawa manoma bashi na kamar yadda gwamnatin tarayya ta kadamar, munyi imanin zai cika alkawarin da ya dauka."

Ali ya ce jihar Yobe tana da albarkatu sosai a garuruwan Nguru, Gashua, Geidam, Ngeji, Gadaka/Ngojin da sauransu da ya ce har yanzu ba a cin gajiyarsu kamar yadda ya kamata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel