Ka tabbatar da Tanko Muhammad matsayin alkalin alkalai na din-din-sin - Majalisar Shari'a NJC ta bukaci Buhari

Ka tabbatar da Tanko Muhammad matsayin alkalin alkalai na din-din-sin - Majalisar Shari'a NJC ta bukaci Buhari

Bisa ga shawarar majalisar koli ta shari'a NJC, komai ya kankama domin tabbatar da mukaddashin shugaban Alkalai, Ibrahim Tanko Muhammad, a matsayin Alkali alkalai na din-din-din.

Ana kyautata zaton cewa shugaba Muhammadu Buhari zai karbi shawarar majalisar Shari'a ta kasa. Jaridar The Nation ta bada rahoto.

Amma rahoto ya nuna cewa Buhari na tantaman karbar shawarar matsaliyar kolin kan cewa a yiwa tsohon alkalin alkalai, Walter Onnoghen, ritayar dole maimakon hukunta shi.

Buhari ya gana da mataimakinsa, Yemi Osinbajo, kan al'amarin kafin shillawa kasar Urdu jiya, kana yana neman shawarwarin lauyoyi kan wannan al'amari.

Majalisar koli NJC ta wanke Alkali Muhammad daga zargin laifin da ake yi masa na gabatar da kansa domin rantsar da shi ba bisa ka'ida ba.

KU KARANTA: Za a yi wa mutumin da ya kashe musulmai 50 a New Zealand gwajin kwakwalwa

Wani babban jami'in gwamnati wanda aka sakaye sunansa ya bayyana cewa Buhari na shakkan karbar shawarar NJC na yi wa Alkali Walter Onnoghen ritaya saboda yin hakan zai bashi daman samun cikakken yanci, kudin ritaya da fansho.

Mun kawo muku rahoton cewa majalisar koli ta bangaren shari'a NJC ta baiwa shugaban Muhammadu Buhari shawarar yiwa dakataccen alkalin alkalai, Walter Nkanu Onnoghen, ritayan dole.

Bayan tattaunawar da sukayi kan tuhumce-tuhumcen da hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC tayi masa, mambobin NJC sun zanna ranar Laraba kuma sun yi ittifakin cewa Walter Onnoghen bai cancanci cigaba da zama Alkali ba.

Kana majalisar NJC ta yanke shawarar cewa Alkali Tanko Mohammad bai aikata laifin komai ba na gabatar da kansa gaban shugaban kasa domin rantsar da shi matsayin mukaddashin CJN ba tare da izininta ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel