Okorocha zai san makomarsa a ranar Laraba yayinda INEC ta kafa kwamiti

Okorocha zai san makomarsa a ranar Laraba yayinda INEC ta kafa kwamiti

Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta kaddamar da wani kwamiti akan zaben sanata na Imo ta arewa.

Hukumar INEC ta bayyana hakan ne a wani jawabin manema labarai dauke da sa hannun Mista Festus Okoye, kwamishinan INEC na kasa kan ilimantar da masu zabe.

Akan zaben jihar Rivers da aka kammala, Okoye yace za a sake gudanar da zabe a ranar 13 ga wannan watan.

A nata bangaren kan zaben Rivers da aka kammala, hukumar INEC ta nuna gamsuwarta akan sakamakon zabe.

Okorocha zai san makomarsa a ranar Laraba yayinda INEC ta kafa kwamiti
Okorocha zai san makomarsa a ranar Laraba yayinda INEC ta kafa kwamiti
Source: Twitter

Yace, “hukumar ta nuna gamsuwarta da sakamakon zaben kuma ta yabi hukumomin tsaro akan kwarewarsu. Wanda ya yabbatar da zaben cikin kwanciyar hankali.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin Najeriya ta karyata batun rufe ofisoshin jakadancinta

“Duk da haka ya yabi jam’iyyun siyasa, jami’in zabe daga kasashen ketare, masu ruwa da tsaki da kuma mutanen jihar Rivers kan goyon baya da fahimtar juna wanda yayi sanadiyyar tabbatar da kammala aikin.

Duk da haka, za a sake gudanar da zabbuka a wasu yankunan jihar a ranar 13 ga watan Afrilu, 2019, bisa tsarin da hukumar ya sanar.

A wani lamari na daban, Legit.ng ta rahoto Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa sabbin mutanen da za a ba mukaman siyasa za su fuskanci gwajin kwaya kafin a basu mukamai a sabon gwamnatinsa.

Ya kuma bayyana cewa za a rushe majalisar da dukkanin nade-naden siyasa a ranar 29 ga watan Mayu, 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel