Fafutukar neman shugabancin majalisa: Lawan ya gana da gwamnonin APC

Fafutukar neman shugabancin majalisa: Lawan ya gana da gwamnonin APC

Daga cikin tattaunawa da yake yi da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki kan kudirinsa na neman shugabancin majalisar dattawa, Shugaban masu rinjaye a majalisa, Sanata Ahmad Lawan, ya gana da gwamnonin APC hudu a Abuja, jaridar Thisday ta ruwaito.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da manyan sanatoci biyu, Mohammed Goje da Ali Ndume wadanda ke hararar kujerar Shugabancin majalisar suka fara tattaunawa kan yiwuwar yin aiki tare.

An tattaro cewa ganawar da Lawan yayi da gwamnonin ya gudana ne a daren ranar Talata a karkashin ikon gwamnan jihar Yobe, Alhaji Ibrahim Geidam, wanda a yanzu shima zababben sanata ne.

Rahoton ya nuna cewa sun yi ganawar ne domin mara wa kudrin Lawan baya a matakin kungiyar gwamnonin APC.

Fafutukar neman shugabancin majalisa: Lawan ya gana da gwamnonin APC

Fafutukar neman shugabancin majalisa: Lawan ya gana da gwamnonin APC
Source: Twitter

Bincike ya nuna cewa taron tattaunawar, wanda ya gudana a wani gidan saukar baki a Aso Drive ya samu halartam Shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya, Gwamna Abdulaziz Yari na jihar Zamfara, wanda a yanzu shima zababben sanata ne; Gwamna Nasir el-Rufao na jihar Kaduna da kuma takwaransa na jihar Adamawa, Mohammed Bindow.

KU KARANTA KUMA: Wata kungiya ta je majalisa, ta nemi Goje ya kaddamar da kudirinsa na takarar shugabancin majalisar dattawa

An tattaro cewa Geidam, wanda ya kasance gwamnan jihar da Lawan ya fito, ya kira taron ne domin marawa kudirin Lawan baya na son jagorancin majalisar dattawa na tara.

Wata mjiya ta bayyan cewa Lawan yayi amfani da dammar wajen neman goyon bayan gwamnonin APC da na zababbun sanatocin jam’iyyar a jihohi 22 gabannin rantsar da yan majalisar a watan Yuni.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel