Yanzu-yanzu: Gobara ta kone shaguna 8 a Kano

Yanzu-yanzu: Gobara ta kone shaguna 8 a Kano

- Gobara mai karfi ta cinye shaguna takwas a jihar Kano

- Gobarar wacce ta shi a safiyar yau dinnan da misalin karfe 6:15 ta yi barna mai yawa bayan kone shaguna takwas din

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta sanar da cewar shaguna takwas sun kone sanadiyyar wata gobara da ta kama a titin Katsina Road, da ke karamar hukumar Ungogo, cikin birnin Kano.

Alhaji Saidu Mohammed, mai magana da yawun hukumar kashe gobarar, shine ya tabbatar da hakan ga kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN), ya bayyana cewa gobarar ta kama da misalin karfe 6:15 na safe.

Yanzu-yanzu: Gobara ta kone shaguna 8 a Kano

Yanzu-yanzu: Gobara ta kone shaguna 8 a Kano
Source: Depositphotos

"Mun samu kiran gaggawa a ofishin mu na Dawanau daga wani mutum mai suna Aliyu Mansir, da misalin karfe 6:15 na safe, inda ya ke sanar damu cewa gobara ta kama a kan titin Katsina Road.

"Bayan mun samu wannan sanarwar muka tura jami'an mu wurin da misalin karfe 6:58 domin kashe gobarar, kada ta yi barna da yawa," in ji mai magana da yawun hukumar.

KU KARANTA: Hanyoyi guda 6 da za a bi don samawa kai sassaucin zafi a wannan lokaci

Ya kara da cewa suna gabatar da bincike akan ainahin dalilin da ya sa wutar ta kama.

Ba wannan ne karo na farko da ake samun matsala ta gobara ba a jihar ta Kano, sai dai har yanzu da yawa daga cikin gobarar da ta ke kama wa ba a san dalilin kamawarsu ba.

A shekarun baya an yi ta fama da matsalar gobara a jihar ta Kano, musamman ma a manyan kasuwannin ciki da wajen jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel