Ganduje zai rushe majalisarsa a 29 ga watan Mayu, za a yi wa sabbin shiga gwajin kwaya

Ganduje zai rushe majalisarsa a 29 ga watan Mayu, za a yi wa sabbin shiga gwajin kwaya

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa sabbin mutanen da za a ba mukaman siyasa za su fuskanci gwajin kwaya kafin a basu mukamai a sabon gwamnatinsa.

Ya kuma bayyana cewa za a rushe majalisar da dukkanin nade-naden siyasa a ranar 29 ga watan Mayu, 2019.

Za a rantsar da Ganduje a ranar 29 ga watan Mayu, bayan yayi nasarar lashe zaben gwamnan jihar da ya gudana a ranar 29 ga watan Maris karo na biyu.

Yayinda yake magana a lokacin da ya karbi bakuncin tawagar kwamitin shugaban kasa akan miyagun kwayoyi wanda Janar Mohammad Buna Marwa (mai ritaya) ya jagoranta a gidan gwamnatin Kano, Ganduje ya karfafa cewa daga ranar 29 ga watan Mayu, sabbin nade-naden mataimaka na musamman, shuwagabannin hukumomi da kwamishinoni zasu fuskanci gwajin kwayoyi.

Ganduje zai rushe majalisarsa a 29 ga watan Mayu, za a yi wa sabbin shiga gwajin kwaya

Ganduje zai rushe majalisarsa a 29 ga watan Mayu, za a yi wa sabbin shiga gwajin kwaya
Source: Depositphotos

Bayan damuwa da yanda ake amfani da miyagun kwayoyi a Kano, gwamnan ya karfafa cewa gwamnatinsa ta kammala shirye-shirye don kafa cibiyar yaki da miyagun kwayoyi.

Yace kafa cibiyan zai tallafa ma sauran cibiyoyin wajen inganta ayyukan shirin gwamnati wanda aka kafa don canja rayuwar masu harka da miyagun kwayoyi a jihar.

KU KARANTA KUMA: Wata kungiya ta je majalisa, ta nemi Goje ya kaddamar da kudirinsa na takarar shugabancin majalisar dattawa

Shugaban kwamitin shugaban kasa akan miyagun kwayoyi, Janar Marwa ya fada ma gwamnan cewa yankin Arewacin Najeriya na da yara kimanin miliyan 14 da suka bar makaranta wanda a cikinsu miliyan 10 almajirai ne.

Marwa, wanda ya nuna damuwar shi akan yaran almajirai wadanda ake shigar dasu harkar miyagun kwayoyi, ya bukaci gwamnan jihar da ya kaddamar da cibiyar ilimantarwa ga yara.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel