Gwamnatin Najeriya ta karyata batun rufe ofisoshin jakadancinta

Gwamnatin Najeriya ta karyata batun rufe ofisoshin jakadancinta

- Gwamnatin tarayya ta karyata rahotonnin da ke cewa za ta rufe wasu ofisoshin jakadancinta guda 80 cikin 110 da take da su a kasashen duniya

- Ta bayyana rahoton a matsayin kanzon kurege mara tushe

- An dai yi zargin cewa Najeriya za ta rufe su ne saboda ba ta da halin ci gaba da gudanar da su

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta karyata rahotonnin da ke yawo kan cewa za ta rufe wasu ofisoshin jakadancinta guda 80 cikin 110 da take da su a kasashen duniya.

A ranar Alhamis, 4 ga watan Afrilu ne dai aka wayi gari da rahotonnin cewa kasar na kokarin rufe 80 daga cikin ofisoshin jakadancinta da ke fadin duniya.

Rahotannin sun kawo cewa Najeriya za ta rufe su ne domin ba ta da halin ci gaba da gudanar da su. An kuma ce kasafin kudin baya-bayan nan ya ware kudin da za a gudanar da ayyukan ofisoshi talatin ne kawai.

Gwamnatin Najeriya ta karyata batun rufe ofisoshin jakadancinta

Gwamnatin Najeriya ta karyata batun rufe ofisoshin jakadancinta
Source: UGC

To sai dai wani jami'an gwamnatin kasar ya ce rahoton ba shi da wani tushe ballantana makama, kwai dai kanzon kurege ne.

KU KARANTA KUMA: Kotun sauraron kararrakin zaben Kano ta tauna tsakuwa ga yan siyasa

A ranar Laraba ne dai kwamitin harkokin kasashen waje na majalisar dattawan kasar ya bayyana cewa ofisohin jakadancin kasar a fadin duniya na cikin wani mummunan yanayi, inda kuma kwamitin ya zargi gwamnatin tarayyar kasar da yin watsi da su.

A wani lamari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa Manajan Darakta na kamfanin man fetur na Najeriya (NNPC), Maikanti Baru, ya ce kamfanin za ta cigaba da gabatar da binciken man fetur a arewa har sai ya cimma burinsa na samun man fetur isasshe a arewa.

A lokacin da yake ganawa da manema labarai a Kaduna, shugaban kamfanin ya ce, cigaba da binciken zai taimakawa kamfanin wajen samo iskar gas da ke ajiye a yankin tun shekarar 1999.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel