Za a cigaba da nemo man fetur a Arewa - Maikanti Baru

Za a cigaba da nemo man fetur a Arewa - Maikanti Baru

- Akwai yiwuwar nan da wata daya za a iya samu isasshen man fetur a arewa

- Manajan kamfanin shine ya tabbatar da hakan maneman labarai

- Ya ce kamfanin zai cigaba da aiki har sai ya cimma burin shi na samar da man fetur a yankin

Manajan Darakta na kamfanin man fetur na Najeriya (NNPC), Maikanti Baru, ya ce kamfanin za ta cigaba da gabatar da binciken man fetur a arewa har sai ya cimma burinsa na samun man fetur isasshe a arewa.

A lokacin da yake ganawa da manema labarai a Kaduna, shugaban kamfanin ya ce, cigaba da binciken zai taimakawa kamfanin wajen samo iskar gas da ke ajiye a yankin tun shekarar 1999.

Za a cigaba da hako man fetur a Arewa - Maikanti Baru
Za a cigaba da hako man fetur a Arewa - Maikanti Baru
Source: UGC

A cewarshi, kamfanin ya na aiki a yankin kogin Kolmani, sannan akwai tabbacin cewa za a cimma burin abinda ake nema, sannan ya kara da cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci kamfanin ya kara dagewa da binciken a yankin na kogin Kolmani

Ya ce a halin yanzu kamfanin ya yi nisa da aikin hakar iskar din, in da bai fi kashi 20 cikin 100 ya rage ba yanzu, ya kara da cewa akwai yiwuwar za a samu iskar gas din a cikin watan Mayu da za a shiga.

KU KARANTA: Wasu daliban sakandare sun kirkiro wata fasaha da za ta rage cunkoson motoci a Najeriya

"Dalilin da ya sa muke haka wannan rijiyar, shine akwai yiwuwar zamu samu iskar gas da aka ajiye tun shekarar 1999 a nan kogin Kolmani, kuma cikin ikon Allah komai yana tafiya yanda ya kamata."

Idan ba a manta ba tun hawan Shugaban kasa Muhammadu Buhari a shekarar 2015 ya ke kokarin ganin ya samar da man fetur a yankin arewa ta re da haddin guiwar kamfanin man fetur na kasa (NNPC) , a yanzu haka dai akwai bayanai da su ke nuna an samu man fetur din a wani yanki a jihar Bauchi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel