Wata kungiya ta je majalisa, ta nemi Goje ya kaddamar da kudirinsa na takarar shugabancin majalisar dattawa

Wata kungiya ta je majalisa, ta nemi Goje ya kaddamar da kudirinsa na takarar shugabancin majalisar dattawa

Wata kungiyar matasa a arewa maso gabas tayi kira ga Sanata Danjuma Goje, da ya bayyana wa al’umma ra’ayinsa na takarar mukamin shugaban majalisar dattawa.

Kungiyar wacce ta samu jagorancin wani Bello Ambo daga jihar Bauchi, wanda ya shiga harabar majalisar ya riko takardu da ke neman dan majalisan ya bayyana ra’ayinsa akan mukamin shugaban majalisa.

Mambobin kungiyar sun shigo harabar suna wakoki da ke bukatar dan majalisar ya bayyana niyyarsa nan ba da dadewa ba saboda yarda da suka yi kan tsarin shugabancinsa.

Ambo, ya bayyana ma manema labarai cewa tsayar da Sanata Ahmad Lawan (APC-Yobe) da shugabancin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa da kuma bayyana ra’ayin da Sanata Ali Ndume yayi (APC-Borno) yayi duk baza su hana Goje bayyana nashi ra’ayin ba.

Wata kungiya ta iso majalisa, ta nemi Goje ya kaddamar da kudirinsa takarar shugabancin majalisar dattawa

Wata kungiya ta iso majalisa, ta nemi Goje ya kaddamar da kudirinsa takarar shugabancin majalisar dattawa
Source: Depositphotos

Shugaban kungiyar yace Goje ya cancanci mukamin, kuma kada ya bata lokaci wajen bayyana kudirinsa.

Yace takardun dan majalisan sun nuna cancantan shi, bayan kasancewarsa gwamnan har na tsawon shekaru takwas tsakanin 2003 da 2011, ya kuma kasance a majalisa tun bayan saukarsa daga mukamin gwamna.

KU KARANTA KUMA: Ba gudu ba ja da baya kan kudirina na neman Shugabancin majalisar dattawa - Ndume

Wani shugaban kungiyar reshen jihar Yobe, Mista Abdul Salah, yace ko da yake Lawan ya kasance daga jiharsa, ya yarda da goje har idan za a bashi daman.

Akan cewa an dauki nauyin kingiyar ne, Saleh yace babu wanda ya dauki nauyin kungiyar kuma basu kai ga haduwa da Sanata Goje ido da ido ba.

Goyon bayan da suka nuna ga Goje don shiga takaran na zuwa ne yan sa’o’i 48 bayan Sanata Ali Ndume ya lissafa ajanda guda tara idan aka zabe shi a matsayin shagaban majalisar dattawan.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel