Nigeria na rasa N400bn a shekara wajen neman magani a kasashen waje - Buhari

Nigeria na rasa N400bn a shekara wajen neman magani a kasashen waje - Buhari

- Shugaba Muhamadu Buhari ya koka kan yadda 'yan Nigeria ke kashe makudan kudade a kowacce shekara wajen neman magani a kasashen ketare

- Buhari ya yi kira ga mahalarta taron kwas din da su gano hanyoyin magance gibi da matsalolin da ake samu a cibiyar, domin bunkasa sa hannun jari a ilimin kasar

- Ya bayyana cewa gwamnatinsa ta samar da N55.1bn a 2018 domin sa jari a asibitocin kasar kamar yadda yake a dokar lafiya ta 2014

Shugaban kasar Nigeria, Muhamadu Buhari ya koka kan yadda 'yan Nigeria ke kashe makudan kudade a kowacce shekara wajen neman magani a kasashen ketare.

Shugaban kasar ya bayyana damuwarsa a yayin kaddamar da kwas na manyan shuwagabanni na cibiyar nazarin tsare tsare ta kasa (NIPSS).

Buhari, wanda ya samu wakilcin Simon Lalong, gwamnan jihar Filato, ya yi kira ga mahalarta taron kwas din da su gano hanyoyin magance gibi da matsalolin da ake samu a cibiyar, domin bunkasa sa hannun jari a ilimin kasar.

KARANTA WANNAN: Wata miyar sai a makwafta: Kasar Zimbabwe ta haramta dukan yara 'yan kasa da shekaru 18

Nigeria na rasa N400bn a shekara wajen neman magani a kasashen waje - Buhari

Nigeria na rasa N400bn a shekara wajen neman magani a kasashen waje - Buhari
Source: UGC

Ya karfafi guiwarsu akan ci gaba da bincike da neman karin ilimi kan yadda kasashen Afrika, Asia, Europe da Amurka ke daukar nauyin bunkasa fannin lafiyarsu, da kuma yadda binciken nasu zai amfani kasar.

Shugaban kasar ya ce gwamnatinsa ta dukufa wajen ganin ta bunkasa fannin lafiyar kasar da kuma rage yawan kudaden da ake kashewa wajen neman lafiya a wasu kasashe, yana mai cewa gwamnatinsa ta samar da N55.1bn a 2018 domin sa jari a asibitocin kasar kamar yadda yake a dokar lafiya ta kasa da aka sawa hannu a 2014.

Issac Adewole, ministan Ilimi, ya gabatar da makala akan ilimi a wajen taron kwas din, yayin da mai shari'a Yakubi Dakwak, babban jojin jihar Filato, ya jagoranci rantsar da sabbin mahalarta taron guda 66.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel