Baki shike yanka wuya: An kama wani babban dan Kwankwasiyya saboda zargin batanci

Baki shike yanka wuya: An kama wani babban dan Kwankwasiyya saboda zargin batanci

Jami’an hukumar tsaro ta DSS sun cafke wani matashi a jahar Kano dan kwankwasiyya dake bakar adawa da gwamnatin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, Salisu Hotoro, a ranar Alhamis, 4 ga watan Afrilu.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito jami’an sun kama Salisu a gidansa dake unguwar Hotoro, cikin garin Kano sakamakon batanci da ake zarginsa da yi ga tsohon shugaban hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa na Najeriya, NPA, Aminu Dabo.

KU KARANTA: Buhari na kan cika ma yan Najeriya alkawarin daya daukan musu – fadar shugaban kasa

Baki shike yanka wuya: An kama wani babban dan Kwankwasiyya saboda zargin batanci

Salisu
Source: UGC

Shi dai Aminu Dabo ya gamu da suka ne daga mabiya darikar Kwankwasiyya biyo bayan zancen da yayi na cewa shine yake daukan nauyin yan Kwankwasiyya a baya, kafin ficewarsa daga darikar ya koma jam’iyyar APC.

Kaakakin dan takarar gwamnan jahar Kano a inuwar jam’iyyar PDP, Abba Yusuf, Sanusi Dawakin-Tofa ya tabbatar da aukuwar lamarin a shafinsa na kafar sadarwar zamani ta Facebook, inda yace “Jami’an DSS sun kama Salisu Hotoro a matsayinsa na mai sukar gwamnati kuma dan Kwankwasiyya.

“Jami’an tsaron sun ci mutuncin Salisu tare da wulakantashi, inda suka daura masa ankwa a kafafuwa da hannayensa, sa’annan suka yo awon gaba da shi, har yanzu babu wanda ya san inda suka kai shi, muna Allah wadai da wannan barazanar da makiya Dimukradiyya suke mana.” Inji shi.

Bugu da kari Kaakakin yace hakan wani mataki ne rufe musu baki daga caccakar gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnatin Ganduje, shi yasa suke kai hare hare akansa da sauran mabiya Kwankwasiyya, musamman masu rubuce rubuce a kafafen sadarwar zamani.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel