Kotun sauraron kararrakin zaben Kano ta tauna tsakuwa ga yan siyasa

Kotun sauraron kararrakin zaben Kano ta tauna tsakuwa ga yan siyasa

Kotun da ke sauraron kararrakin zaben Gwamna da na yan majalisar jihar Kano ta ja kunnen yan siyasa, ta bayyana cewa ba za ta amince da yi mata katsalandan daga kowa ba a lokacin da ta fara zamanta.

Jagoran kotun, mai shari’a Nayai Aganaba, ne ya yi wannan jan kunnen a yayinda yake kaddamar da wakilan kotun a ranar Alhamis, 4 ga watan Afrilu a Kano.

Ganaba wanda ya kaddamar da kwamitin mutum uku wadanda suka hada dashi kansa, da wasu mutane biyu, Mai shari’a Ashu Augustine Ewah da Mustapha Tijjani, ya bayyana cewa ba za su lamunci wani daga waje ya yi masu katsalandan ba a kan dukkanin shari’an zaben da za su yi.

Har ila yau, ya gargadi Lauyoyin da za su yi shari’an zaben, da su bi a sannu kamar yanda dokar aikin su ta tanadar.

Kotun sauraron kararrakin zaben Kano ta tauna tsakuwa ga yan siyasa

Kotun sauraron kararrakin zaben Kano ta tauna tsakuwa ga yan siyasa
Source: Twitter

Ya kuma bukaci Lauyoyin da kar wani abu ya tunzura su a lokacin da suke aikin na su, shugaban kotun ya ce, “Kamar yanda ku ka sani, ‘Yan siyasa duk abokanan juna ne, haka suke tsallakawa daga wannan Jam’iyya zuwa waccan."

KU KARANTA KUMA: Ba gudu ba ja da baya kan kudirina na neman Shugabancin majalisar dattawa - Ndume

Aganaba, ya yi gargadin cewa kotun ba wajen shan shayi bane, kotu ba wuri ne ba na wasa, don haka, ba wani dalilin da zai sanya Lauyoyi su rika rigima da junan su a bayyane.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel