Wata miyar sai a makwafta: Kasar Zimbabwe ta haramta dukan yara 'yan kasa da shekaru 18

Wata miyar sai a makwafta: Kasar Zimbabwe ta haramta dukan yara 'yan kasa da shekaru 18

- Kotun dokokin kasar Zimbabwe ta haramta dukan 'yan kasa da shekaru 18 da bulala, da sunan yi masu hukunci akan wani laifi da suka aikata

- Yayin da halayye ke canjawa, da yawan iyaye a Zimbabwe na ci gaba da kallon dukan yara da bulala shi ne kadai hanyar horas da 'yayansu

- Hukuncin ya zo bayan da wai dan kasa da shekaru 15 da ake zarginsa da yiwa wata yarinyar mai shakru 14 fyade ya kalubalanci wani hukunci da aka yi masa na bulalu ukku

Kotun dokokin kasar Zimbabwe ta haramta dukan 'yan kasa da shekaru 18 da bulala, da sunan yi masu hukunci akan wani laifi da suka aikata. Masu shari'a guda tara ne suka yanke wannan hukuncin na cewa dukan 'yan kasa da shekaru 18 ya sabawa dokar kasar.

Sun bayyana cewa irin wannan hukuncin tamkar cin zarafi ne, rashin imani da kuma wuce ka'idar hukunci.

Yayin da halayye ke canjawa, da yawan iyaye a Zimbabwe na ci gaba da kallon dukan yara da bulala shi ne kadai hanyar horas da 'yayansu, a cewar wani rahoto na Shingai Nyoka na BBC.

KARANTA WANNAN: Makiyaya 'yan ta'adda ne, ya zama tilas Buhari ya ayyana hakan - Onitiri

Wata miyar sai a makwafta: Kasar Zimbabwe ta haramta dukan yara 'yan kasa da shekaru 18

Wata miyar sai a makwafta: Kasar Zimbabwe ta haramta dukan yara 'yan kasa da shekaru 18
Source: Twitter

Kasar Zimbabwe ta amince da dukan yara da bulala amma idan maza ne 'yan kasa da shekaru 18, karkashin dokar tsarin tabbatar da aikata laifukan ta'addanci kuma dole hukuncin ya kasance a mizanin hankali.

Sai dai, masu shari'ar sun gano cewa hakan ya sabawa sashen dokar kasar na shekarar 2013, da ta bayyana cewa babu wani mutum da ya cancanci "rashin tausayi, cin zarafi ko kuma hukunci mai tsanani".

Hukuncin ya zo bayan da wai dan kasa da shekaru 15 da ake zarginsa da yiwa wata yarinyar mai shakru 14 fyade ya kalubalanci wani hukunci da aka yi masa na bulalu ukku.

Sai dai har yanzu ba a bayyanawa jama'a cikakken bayani kan shari'ar yaron ba.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel