Ba gudu ba ja da baya kan kudirina na neman Shugabancin majalisar dattawa - Ndume

Ba gudu ba ja da baya kan kudirina na neman Shugabancin majalisar dattawa - Ndume

Tsohon Shugaban masu rinjaye kuma daya daga cikin manyan yan takarar kujerar Shugaban majalisar dattawa, Saanata Mohammed Ali Ndume, ya sha alwashin ci gaba da tseren har sai an gudanar da zaben shugabancin majalisar dokokin kasar, imma ya ci ko ya fadi.

Sanata Ndume, wanda ya bayyana zuciyarsa akan lamarin a gaban majalisar dattawa a Abuja a jiya Alhamis, 4 ga watan Afrilu, ya bayyana cewakada a fassara jajircewarsa na takarar kujerar a matsayin rashin girmamawa ga matsayar jam’iyyarsa ta All Progressives Congress (APC) wacce ta rigada ta tsayar da Shugaban masu rinjaye a majalisa, Sanata Ahmed Lawan a matsayin zabinta na shugabancin majalisar.

Ba gudu ba ja da baya kan kudirina na neman Shugabancin majalisar dattawa - Ndume

Ba gudu ba ja da baya kan kudirina na neman Shugabancin majalisar dattawa - Ndume
Source: Facebook

Ndume ya bayyana cewa kamar yadda a shirye yake ya yi biyayya ga umurnin APC, gaskiyar Magana shine yana da yancin yin takarar kowani kujera a majalisar dattawa.

KU KARANTA KUMA: Makiyaya 'yan ta'adda ne, ya zama tilas Buhari ya ayyana hakan - Onitiri

Dan majalisar wanda ya fito daga jihar Borno ya bayyana cewa baya adawa da raba matsayin shugabancin majalisar ga yanki, amma abunda yake adawa dashi shine batun hana wani mutun takarar wani kujera.

A matsayinsa na zababben sanata, Ndume ya bayyana cewa yana da yancin takarar kowani matsayi kuma zai ci gaba da adawa da hukuncin m’iyyar na tursasa wani dan takara akan shi da majalisar dattawan.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel