Makiyaya 'yan ta'adda ne, ya zama tilas Buhari ya ayyana hakan - Onitiri

Makiyaya 'yan ta'adda ne, ya zama tilas Buhari ya ayyana hakan - Onitiri

- An yi kira ga shugaba Buhari da ya ayyana makiyaya a matsayin 'yan ta'adda sakamakon kara yawaitar kashe kashen rayukan da basu ji ba basu gani ba

- Chief Adesunbo Onitiri ya ce ya zama wajibi gwamnatin tarayya ta tashi tsaye tare da kawo karshen ta'addancin makiyayan kafin su kashe kowa a kasar

- A cewar Onitiri, a yanzu makiyaya sun fara komawa ababen tsoro da hatsari ga jama'a fiye da Boko Haram da ke a shiyyar Arewa maso Gabas

An yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya ayyana makiyaya a matsayin 'yan ta'adda sakamakon kara yawaitar kashe kashen rayukan da basu ji ba basu gani ba, da sunan cewa kungiyar makiyayan na kiwon dabbobinsu, wanda a hannu daya ke zama babbar barazana ga al'ummar kasar.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga dan takarar sanatan Legas ta tsakiya karkashin jam'iyyar PDP, Chief Adesunbo Onitiri da ya rabawa manema labarai a Legas a ranar Alhamis, yana mai cewa ya zama wajibi gwamnatin tarayya ta tashi tsaye tare da kawo karshen ta'addancin makiyayan kafin su kashe kowa a kasar.

A cewar Onitiri, a yanzu makiyaya sun fara komawa ababen tsoro da hatsari ga jama'a fiye da Boko Haram da ke a shiyyar Arewa maso Gabas saboda yanzu ana samun makiyayan a dukkanin fadin kasar kuma suna kai farmaki ga dukkanin wanda suka ci karo da shi.

KARANTA WANNAN: Da zafinsa: Sanata Kabiru Gaya ya tsaya takarar mataimakin shugaban majalisar dattijai

Makiyaya 'yan ta'adda ne, ya zama tilas Buhari ya ayyana hakan - Kungiya

Makiyaya 'yan ta'adda ne, ya zama tilas Buhari ya ayyana hakan - Kungiya
Source: UGC

"Kamar yadda jaridun kasar suka ruwaito, makiyayan, wadanda wasunsu ake zargin cewa Fulani ne, sun kashe jami'in rundunar sojin sama, matuki a jihar Edo, 'yan sanda sun cafke makiyaya hudu bisa laifinsu da garkuwa da wani babban malamin majami'ar Katolika da ke Enugu, makiyaya da ake zargin Fulani ne sun kashe wata mata ta hayar dukanta.

"Ko a 2016, wasu makiyaya sun kai hari a garin Agatu da ke jihar Benue inda suka kashe mutane 16. Haka zalika a jihar Benue, an kashe sama da mutane 100 da har hakan ya jawo hankulan kasashen ketare. Bai kamata dukkanin wadanda abubuwa su tafi a banza ba," a cewar dan takarar jam'iyyar PDP.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel