An kori dan sandan da ya kashe Kolade Johnson daga aiki

An kori dan sandan da ya kashe Kolade Johnson daga aiki

- Hukumar 'yan sandan jihar Legas ta kori dan sandan da ya kashe Kolade Johnson daga aiki

- Sannan ta bayyana cewa ta mika shi ga hukumar gabatar da bincike domin gabatar da kwakkwaran bincike akan shi

Hukumar 'yan sanda ta kori Ogunyemi Olalekan, daya daga cikin 'yan sanda biyu da ake zargin su da harbin Kolade Johnson, a gidan kallon kwallon kafa, a ranar 31 ga watan Maris, a jihar Legas.

An kama Olalekan da laifin kisan a lokacin da aka fara gabatar da shari'ar shi ranar Litinin.

Wani harsashi da ya kauce hanya ya sami marigayin, a dai dai lokacin da jami'an hukumar 'yan sandan suke artabu da 'yan kungiyar asiri a Onipetesi, da ke kan hanyar Legas zuwa Abeokuta, ranar Lahadi.

An kori dan sandan da ya kashe Kolade Johnson daga aiki

An kori dan sandan da ya kashe Kolade Johnson daga aiki
Source: UGC

Lamarin ya haifar da cece-kuce a cikin al'umma wanda ya tilasta hukumar 'yan sanda ta bayyana Olalekan da Godwin Orji, a matsayin wadanda su ka aikata kisan.

A wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, mai magana da yawun hukumar 'yan sandan jihar Legas, Bala Elkana, ya ce hukumar ta samu Olalekan ne kawai da laif, inda ta bayyana Godwin Orji a matsayin wanda bashi da hannu a kisan.

"Jami'an 'yan sandan biyu da ake zargi da harbin Kolade Johnson a ranar 31 ga watan Maris, sun shiga hannu inda a yanzu haka kotu ta ke tuhumar su," in ji Elkana.

Ya cigaba da cewa: "An fara sauraron karar ta su ranar Litinin 01/04/2019, sannan an gama sauraron karar ranar Alhamis 04/04/2019.

KU KARANTA: Wasu daliban sakandare sun kirkiro wata fasaha da za ta rage cunkoson motoci a Najeriya

"A karshen shari'ar an kama Ogunyemi Olalekan, da laifin harbin Kolade Johnson bisa ganganci.

"Babban jami'i mai gudanarwa na hukumar 'yan sandan CSP Indyar Apev, ya kori Olalekan daga aikin shi a matsayin hukuncin da ya da ce da laifin shi.

"Sannan babu wata hujja da ta ke nuna cewa Godwin Orji ya na da laifi, saboda haka kotu ta sallame shi domin ya je ya cigaba da aikin shi."

'Yan sandan sun kara da cewa sun mika Olalekan zuwa ga ma'aikatar binciken manyan laifuka domin yin bincike a kanshi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel