Batun karin farashin litan man fetir karyane – Inji shugaban NNPC

Batun karin farashin litan man fetir karyane – Inji shugaban NNPC

Shugaban hukumar albarkatun man fetir ta kasa, Maikanti Baru ya karyata rahotannin da ake yadawa game da yiwuwar karin farashin litan man fetir, inda yace duk labara ne na kanzon kurege, inji rahoton jaridar Punch.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Baru na cewa duk da yake akwai hukumar dake da alhakin kayyade farashin mai a Najeriya, amma shugaban kasa Muhammadu Buhari yace ba zai yarda da karin farashin mai a yanzu ba.

KU KARANTA: Innalillahi wa inna ilaihi raji’un: Miji ya yi ma matarsa yankan rago a Kano, ya binne gawar

Batun karin farashin litan man fetir karyane – Inji shugaban NNPC

Shugaban NNPC
Source: UGC

Baru ya bayyana haka ne yayin daya halarci kasuwar Duniya ta jahar Kaduna karo na 40 da a yanzu haka yake gudana a garin Kaduna, inda yace sun yi nisa game da batun lalubo ma fetir tare da aikin hakoshi a yankin Arewacin Najeriya.

A jawabinsa, Baru yace zuwa yanzu sun kai tsayin kafa dubu goma da saba’in da biyar a aikin hakar rijiyar mai ta Kolmani dake tsakanin jahar Gombe da jahar Bauchi, inda yace burinsu su kai nisan kafa dubu goma sha hudu da dari biyu da saba’in (14,270) don fara kwasan mai.

A wani labarin kuma, shahararren dan Najeriyan nan da yayi fice a duniya a bangaren kasuwanci, kuma bakar fata da yafi arziki a Duniya, Alhaji Aliko Dangote ya bayyana babban dalilin da yasa bakin talauci yayi ma yankin Arewacin Najeriya katutu.

Attajirin ya kara da cewa Arewa zata iya samun arzikin da yafi arzikin mai daga harkar noma, amma fa sai sun dage wajen ingantawa tare da habbaka noman, kuma hakan zai yiwu ne kadai ta wajen hada kai da kamfanoni masu zaman kansu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Newspaper

Online view pixel