Farawa da iyawa: Kotu ta fatattaki zababben yar majalisa tun kafin ta shiga ofis

Farawa da iyawa: Kotu ta fatattaki zababben yar majalisa tun kafin ta shiga ofis

Kotun daukaka kara dake zamanta a garin Jos na jahar Filato ta tsige sabuwar zababbiyar yar majalisar dokoki mai wakiltar mazabar karamar hukumar Billiri ta gabas, a jahar Gombe, Rabi Daniel yar jam’iyyar PDP.

Bugu da kari majiyar Legit.ng ta ruwaito kotun daukaka karan ta umarci hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, data mika sabon shaidan cin zabe ga Rambi Iyahlah, a matsain halastaccen dan majalisa mai wakiltar mazabar Billiri ta gabas.

KU KARANTA: Babban dalilin da yasa talauci yayi ma Arewa katutu – daga bakin Dangote

An soma wannan tirka tirka ne tun a yayin gudanar da zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP daya gudana a ranar 4 ga watan Oktoban shekarar 2018, inda Rabi Daniel ta sha kayi a hannun Iyalah bayan ta samu kuri’u 24, shi kuma ya samu 25.

Sai dai abinka da yan siyasan Najeriya, sai baturen shirya zaben fidda gwanin, Jacob Lawal tare da shugaban kwamitin zaben Magaji Lafiaji suka sanar da sunan Rabi Daniel a matsayin wanda ta lashe zaben, kuma jam’iyyar PDP ta amince da hakan.

Wannan ne dalilin da yasa Iyalah ya garzaya gaban kotu don kwatar hakkinsa bayan kwamitin sauraron korafi na jam’iyyar tayi biris da korafin daya shigar, inda a ranar 9 ga watan Janairu yam aka Rabi kara gaban babbar kotun tarayya dake garin Gombe.

Sai dai kotun ta yi fatali da bukatar Iyalah na neman ta tabbatar da shi a matsayin halastaccen wanda ya lashe zaben fidda gwanin, sa’annan ta tabbatar da nasarar Rai Daniel, hakan ne tasa Iyalah ya wuce kotun daukaka kara.

Da yake yanke hukunci, Alkalin kotun daukaka kara, M.N Oniyangi yayi watsi da hukuncin kotun daukaka karan, inda yace Alkalin kotun bai yi adalci ba, don haka ya sanar da Iyalah a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwanin, don haka shine wanda ya dace yah au kujerar da Rabi ke ikirarin ta ci.

Daga karshe kuma Alkalin ya umarci Rabi ta biya Iyalah kudi naira dari, sa’annan ya umarci kwamishinan Yansandan jahar Gombe daya kama Lawal da Lafiaji saboda rawar da suka taka wajen tauye hakkin Iyalah.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel