Buhari ya yi magana a kan zaben 2019, ya kururuta siyasar Najeriya

Buhari ya yi magana a kan zaben 2019, ya kururuta siyasar Najeriya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewar siyasar Najeriya na daga cikin ma fi kyau da tsari a nahiyar Afrika bayan kasar ta cika shekaru 20 cikin mulkin dimokradiyya ba tare da katse wa ba.

Buhari ya fadi hakan ne yayin gabatar da jawabi a wajen bikin yaye daliban jami'ar Legas na zangon karatun shekarun 2017/2018, wanda kuma shine bikin yaye dalibai karo na 50 da jami'ar tayi.

Shugaban hukumar kula da jami'o'in Najeriya, Farfesa Rasheed Yakubu, ne ya wakilci shugaba Buhari a wurin taron bikin yaye daliban.

"Kammala zabukan shekarar 2019 ya tabbatar da cewar Najeriya a matsayinta na kasa ta rungumi siyasa a matsayin tsarin gudanar da gwamnati.

"Gwamnatinmu zata cigaba da kare zabin Najeriya na dawwama a turbar dimokradiyya. Zamu bijiro da tsare-tsare da zasu kara karfafa jijiyoyin dake rike da siyasar Najeriya.

Buhari ya yi magana a kan zaben 2019, ya kururuta siyasar Najeriya

Buhari
Source: Twitter

"Ina mai kara tabbatar maku da cewar gwamnatina ba zata yi wasa ba wajen yin biyayya ga dokokin kasa, yaki da cin hanci, tsaron lafiya da dukiyar jama'a ba da inganta muhimman aiyukan raya kasa ba.

"Ba zamu gaza ba wajen cusa akidar aiki tukuru da riko da gaskiya a zukatan 'yan Najeriya ba, zamu bawa walwalar 'yan Najeriya fifiko fiye da komai.

DUBA WANNAN: Buhari ya gargadi jami'an tsaro a kan cin zalin 'yan Najeriya

"Dole mu hada kai don ganin mun dauki Najeria zuwa mataki na gaba," a cewar shugaba Buhari.

A cewar sa, gwamnatinsa zata cigaba da karfafa gwuiwar jami'o'in Najeriya tare da yin aiki tare da su domin gina dangantaka mai karfi da bangaren masana'antu.

Ya ce zai bayar da gudunmawa domin cike gurbi tsakanin dake tsakanin karatu a rubuce da kuma a zahiri domin samun damar biyan bukatun Najeriya a matsayinta na kasa.

Ya kara da cewa gwamnatinsa tayi imani a kan cewar bayar da ilimi mai nagarta ne kadai zai kawo wa Najeriya cigaba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel