Kotun Abuja ta yanke wa mai basaja a matsayin sojan murka hukuncin dauri a kurkuku

Kotun Abuja ta yanke wa mai basaja a matsayin sojan murka hukuncin dauri a kurkuku

Jastis Danlami Senchi na babbar kotun tarayya dake zamanta a Jabi, Abuja, ta yanke wa wani dan Najeriya mai suna Enabulele Osazee hukuncin dauri na tsawon kwana 30 a gidan yari ko biyan tarar N25,000 saboda yin basaja a matsayin manjo Berneth na rundunar sojin kasar Amurka.

Enabuelele na daga cikin 'yan damfarar yanar gizo (Yahoo boys) da jami'an hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arzikin kasa (EFCC) ta kama a ranar 11 ga watan Mayu na shekarar 2018.

Hukumar EFCC tayi nasarar kama 'yan damfarar ne bayan samun bayanan sirri a kan mummunar sana'ar su ta damfara jama'a ta hanyar yanar gizo (internet).

Kotun Abuja ta yanke wa mai basaja a matsayin sojan murka hukuncin dauri a kurkuku

Kotun Abuja ta yanke wa mai basaja a matsayin sojan murka hukuncin dauri a kurkuku
Source: Twitter

An gurfanar da shi a gaban kotu bisa tuhumarsa da laifin yunkurin aikata zamba.

DUBA WANNAN: 'Yan sanda sun kama mai kera wa da safarar bindigu a Sokoto

"Ana tuhumar ka, Enabulele Osazee, da yunkurin aikata zamba ta hanyar yin basaja a matsayin sojan kasar Amurka, Manjo Barnett Edward, da aka tura kasar Afghanistan aikin tabbatar da zaman lafiya domin damfarar wata mai suna Camela Johnson kudi, dalar Amurka $10,000 a wani lokaci cikin shekarar 2018," kamar yadda a kunshe a cikin takardar tuhumar kotun.

Providence Osimen, Lauyan da yake kare Enabulele, ya nemi kotu ta sasauta wa mai laifin bayan ya amsa laifinsa, yana mai kafa hujja da cewar mai laifin matashi ne kuma ya yi nadamar abinda ya aikata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel