Yunkurin fashi a banki: 'Yan sanda sun harbe 'yan fashi da makami 10

Yunkurin fashi a banki: 'Yan sanda sun harbe 'yan fashi da makami 10

A kalla 'yan fashi da makami 10 ne jami'an 'yan sanda na musamman suka aika kiyama yayin da suke kokarin tuge wani injin fitar da kudi (ATM) a kusa da birnin Sao Paulo na kasar Brazil, kamar yadda rundunar ta sanar.

Rundunar 'yan sandan ta shiga farautar ragowar 'yan fashin da suka gudu bayan sun yi yunkurin yin fashi a wasu bankuna biyu dake birnin Gaurarema mai nisan kilomita 80 a arewa maso gabashin babban birnin kasar Brazil, Sao Paulo.

Wasu daga cikin 'yan fashin sun kutsa cikin bankin tare da yin garkuwa da mutanen da suka samu a cikin bankin. Jami'an 'yan sanda sun kubutar da mutanen bayan 'yan fashin sun gudu.

Kimanin 'yan fashi 25 ne suka kai hari bankunan da sanyin safiyar ranar Alhamis, kamar yadda jawabin rundunar ya bayyana.

'Yan sanda sun samu manyan bindigu bakwai, kanana hudu, sinadarai masu fashewa da rigar garkuwar harsashi yayin da suka gudanar da bincike a yankin da abin ya faru.

Wata na'urar talabijin ta sa-ido a kasar Brazil ta nuna cewar daya daga cikin bankunan da 'yan fashin suka kai wa hari yana kusa da ofshin 'yan sanda. Dayan kuma yana karshen titin da ofishin yake.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel