Bamu yarda ba: APC ta debi kwararun lauyoyi don kallubalantar nasarar PDP a Bauchi

Bamu yarda ba: APC ta debi kwararun lauyoyi don kallubalantar nasarar PDP a Bauchi

Jam'iyyar All Progressives Congress, APC ta gabatar da manyan lauyoyi masu mukamin SAN guda hudu domin kallubalantar nasarar da jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP tayi a zaben gwamna da aka gudanar a jihar Bauchi a cewar Gwamna Mohammed Abdullahi Abubakar.

Bayan dawowarsa garin Bauchi a ranar Laraba, Gwamna Abubakar ya shaidawa magoiya bayansa a ofishin yakin neman zaben APC cewa jam'iyyar za ta garzaya kotu domin kwato nasararsu da PDP ta kwace a jihar.

A baya, Legit.ng ta ruwaito muku cewa Gwamna Abubakar ya amince da shan kaye bayan Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta INEC ta sanar da cewa Sanata Bala Mohammed na jam'iyyar PDP ne ya lashe zaben gwamna a jihar.

DUBA WANNAN: Jerin sunayen sojojin Najeriya da ISWA ta hallaka

Bamu yarda ba: APC ta debi kwararun lauyoyi don kallubalantar nasarar PDP a Bauchi

Bamu yarda ba: APC ta debi kwararun lauyoyi don kallubalantar nasarar PDP a Bauchi
Source: Depositphotos

Duk da cewa a baya gwamnan ya amince da shan kaye inda ya ce kaddara ce daga Allah ya shaidawa magoya bayansa cewa jam'iyyar APC za ta shigar da kara domin kallubalantar nasarar da PDP ta yi.

"Na tafi Abuja a matsayina na dan jam'iyya mai biyaya. Na gana da shugaban jam'iyya na kasa, Na gana da mataimakin shugaban kasa da shugaban kasar Najeriya.

"Dukkan su uku sun ce za su shigar da kara a kotu domin kallubalantar sakamakon zaben gwamna na jiha Bauchi.

"A matsayina na mai biyaya, na amince da matakin da suka dauka. Kowa ya san na amince da kayen da na sha bayan INEC ta fadi sakamakon zabe amma tunda a karkashin jam'iyya nayi takara, jam'iyya ta ce ba ta amince da sakamakon ba," inji shi.

A yayin da ya ke tsokaci a kan matakin da APC da dauka, Shugaban PDP na jihar, Hamza Koshe Akuyam ya ce suna maraba da zuwa kotun da APC za tayi.

"A shirye muke mu hadu da su a kotu. Kotun za ta sake tabbatar da nasarar mu," inji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel