Artabu: Dillalan kwaya sun kone motar jami'an NDLEA a jihar Jigawa

Artabu: Dillalan kwaya sun kone motar jami'an NDLEA a jihar Jigawa

Rundunar 'yan sanda a jihar Jigawa ta tabbatar da mutuwar Abubakar Lawan, wani matashi mai shekaru 25 dake zaune a kauyen Shaiskawa, karamar hukumar Kazaure, bayan ya fada cikin wani dam a kokarin guje wa jami'an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA).

SP Abdu Jinjiri, kakakin rundunar 'yan sanda a jihar Jigawa, ne ya sanar da hakan ga manema labarai a garin Dutse, babban birnin jihar Jigawa, ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 6 na ranar Laraba.

Jinjiri ya bayyana cewar marigayin ya fada cikin ruwan dam din a kokarinsa na guje wa jami'an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi yayin da suka kai wani samame wata mafakar masu dillancin miyagun kwayoyi.

Ya kara da cewa sakamakon mutuwar matashi, wasu fusatattun matasa sun afka wa jami'an NDLEA tare da kone ofishin su.

Artabu: Dillalan kwaya sun kone motar jami'an NDLEA a jihar Jigawa

Jami'an NDLEA
Source: UGC

"A ranar Laraba da misalin karfe 6:00 na yamma, mun samu rahoton cewar wasu fusatattun matasa sun afka ofishin hukumar NDLEA, sun kuma saka masa wuta, a karamar hukumar Kazaure.

"Jami'an mu sun gaggauta zuwa ofishin tare da hana matasan kone ofishin gaba daya, wani jami'in NDLEA guda ya samu rauni," a cewar Jinjiri.

DUBA WANNAN: 'Yan sanda sun kama mai kera wa da safarar bindigu a Sokoto

Sannan ya cigaba da cewa: "jami'an hukumar NDLEA sun kai samame wata mafakar masu sha da sayar da tabar wiwi da kwayoyi a kusa da wani dam, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar wani matashi, Abubakar Lawan, wanda ya fada cikin dam a kokarin gudun kar a kama shi.

"A sakamakon hakan, wasu fusattun matasa suka biyo bayan jami'an, suka cinna wa ofishin su wuta.

"Sai dai, wani sashe ne na ofishin kawai ya kone."

Kakakin ya ce ba a kama kowa ba dangane da faruwar lamarin.

A cewsar sa, rundunar 'yan sanda na gudanar da bincike a kan lamarin domin ganin an kama masu hannu a cikin aikata laifin. (NAN)

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel