Jam'iyyar APC tayi korafi a kan zaben jihohin Bauchi, Sokoto, Adamawa

Jam'iyyar APC tayi korafi a kan zaben jihohin Bauchi, Sokoto, Adamawa

Mataimakin sakataren watsa labarai na jam'iyyar APC na kasa, Yekini Nabena ya yi korafi a kan ingancin zaben raba gardama da aka gudanar a jihohin Bauchi, Sokoto da Adamawa.

Mista Nabena ya ce ko kadan ba a bi dokokin gudanar da zabe ba a yayin gudanar da zaben na raba gardama.

Ya yi wannan furucin ne a ranar Alhamis a Abuja yayin da ya ke hira da manema labarai inda ya ce jam'iyyar APC za ta karbo nasarar ta da aka kwace a kotun sauraron kararrakin zabe.

DUBA WANNAN: Yadda PDP ke kokarin hana Lawan zama shugaban majalisar dattawa - Majiyar APC

Jam'iyyar APC tayi korafi a kan zaben jihohin Bauchi, Sokoto, Adamawa

Jam'iyyar APC tayi korafi a kan zaben jihohin Bauchi, Sokoto, Adamawa
Source: UGC

"A jihar Bauchi, Bala Mohammed ne ya lashe zaben bayan an gudanar zaben raba gardama, a jihar Adamawa kuma Fintiri na jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP ne ya lashe zaben gwamnan.

"A jihar Sokoto kuma, gwamna mai ci a yanzu, Aminu Tambuwal ne ya lashe zaben da kankanin tazarar da akwai alamar tambaya a kai," inji Nabena.

Mista Nabena ya ce ba a gudanar da zabukan raba gardamar ba bisa dokokin zabe da hukumar INEC ta tanadar.

Ya kara da cewa bayan nazarin yadda zabukan raba gardamar suka kasance a jihohin Bauchi, Sokoto da Adamawa ana iya ganin cewa an tafka magudi da sayan kuri'u da razana al'umma.

"Jam'iyyar APC ce ka da fiye da kashi biyu cikin uku na mambobin majalisar dokoki a jihar Bauchi kuma APC ke da rinjaye a jihar Sokoto kamar yadda sakamakon zaben gwamna ya nuna, an tafka magudi a zaben raba gardamar kuma ba a bi dokokin zaben da INEC ta tanada ba.

"Saboda haka, za mu tafi kotu mu kallubalanci sakamakon zaben a kotun sauraron karrakin zabe domin mu karbo nasarar mu da al'umma suka bamu," inji Nabena.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel