Aisha Buhari ta yi alhinin mutuwar tsohuwar shugabar hukumar NAFDAC, Dora Akunyili

Aisha Buhari ta yi alhinin mutuwar tsohuwar shugabar hukumar NAFDAC, Dora Akunyili

Uwar gidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Aisha Buhari, ta yi alhini na tunawa da Marigayiya Farfesa Dora Akunyili, tsohuwar shugaba ta hukumar kula da lafiyar abinci da magunguna ta NAFDAC, National Agency for Food and Drug Administration Control.

Yayin bikin cikar hukumar NAFDAC shekaru 25 da kafuwa, Aisha ta bayyana Marigayiya Dora a matsayin Mace mai jajircewa ta fuskar sadaukar da kai, kwazo da kuma tsayuwar daka wajen yiwa kasar ta bauta.

Aisha Buhari ta yi alhinin mutuwar tsohuwar shugabar hukumar NAFDAC, Dora Akunyili

Aisha Buhari ta yi alhinin mutuwar tsohuwar shugabar hukumar NAFDAC, Dora Akunyili
Source: Getty Images

Aisha Buhari ta ce dangin ta da kuma makusanta sun alkanta kawunansu wajen bayyana sha'awar su cikin harkokin Farfesa Dora musamman yadda ta gudanar da ayyukan ta cikin mafi kololuwar gaskiya da kwarewa a cibiyar tattalin kudin man fetur ta PTF, Petroleum Trust Fund.

Uwar gidan shugaban kasar ta kuma bayyana cewa, Marigayiya Dora yayin rayuwa ta kasance bisa akida ta tsare-tsare da manufofin gwamnatin shugaban kasa Buhari musamman a bangaren yaki da cin hanci da rashawa.

KARANTA KUMA: Babban Hasafi: Mai kudin Duniya, Jeff Bezos, ya saki Matarsa

Yayin ci gaba da kwarara mata yabo sakamakon kwazo da ta yi wajen shimfida tsare-tsare masu tabbatar da kyakkyawar makoma a hukumar NAFDAC, Aisha ta yi addu'o'i na neman Mai Duka ya jikan Marigayiya Dora wadda ta kasance Ministar sadarwa a lokacin rayuwar ta.

Kamfanin dillancin labarai na kasa ya ruwaito cewa, Marigayiya Dora ta samu kyautatuttuka tare da lashe lambar yabo a nan gida Najeriya da kuma kasashen duniya sakamakon muhimmiyar rawa da ta taka wajen tabbatar da ingancin masa'antun magunguna.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel