Osinbajo ya gana da tsohon Firai Ministan Birtaniya, Tony Blair

Osinbajo ya gana da tsohon Firai Ministan Birtaniya, Tony Blair

Da sanadin kafar watsa labarai ta The Punch mun samu cewa, mataimakin shugaban kasar Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo, ya kebance tare da tsohon Firai Ministan Birtaniya, Tony Blair a fadar shugaban kasa ta Villa da ke birnin Abuja.

Osinbajo ya gana da tsohon Firai Ministan Birtaniya, Tony Blair

Osinbajo ya gana da tsohon Firai Ministan Birtaniya, Tony Blair
Source: UGC

Sai dai bayan ganawar su ta sirrance, ba bu wata hira da ta gudanar tsakanin su tare da manema labarai kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito.

Bayan ga kasancewar sa shugaban jam'iyyar adawa ta Labour Party tsakanin shekarar 1994 zuwa 1997 a kasar Birtaniya, Mista Blair ya jagorancin kasar a matsayin Firai Minista daga shekarar 1997 zuwa 2007.

A halin yanzu tsohon Firai Ministan ya kasance shugaban gidauniyar Tony Blair Africa Governance Initiative, wata gidauniya mai zaman kanta da aka assasa domin bayar da tallafi na inganta harkokin gwamnati.

KARANTA KUMA: Alkalin Alkalai Onnoghen ya yi murabus - Shafin yanar gizo ya yi ikirari

A cewar hadimi na musamman ga Mataimakin shugaban kasa a kan harkokin sadarwa, gidauniyar tsohon Firai Ministan Birtaniya tare da hadin gwiwar gidanuniyar Bill and Melinda Gates, za su shige gaba wajen bunkasa rawar fadar shugaban kasa domin habakar tattalin arziki.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel