Alkalin Alkalai Onnoghen ya yi murabus - Shafin yanar gizo ya yi ikirari

Alkalin Alkalai Onnoghen ya yi murabus - Shafin yanar gizo ya yi ikirari

Kwana guda bayan da cibiyar shari'a ta Najeriya NJC, National Judicial Council, ta bayar da shawarar tursasa dakataccen Alkalin Alkalai na Najeriya, Walter Onnoghen ya ajiye aiki yayin da aka tabbatar da zargin sa na laifin rashin yiwa doka da'a, mun samu cewa ya yi murabus na sauka daga mukamin sa.

A yayin da ake ci gaba da takkadama akan zargin Onnoghen da laifin yiwa dokokin kasar nan karan tsaye ta hanyar rashin bayyana dukiyar da ya mallaka, rahotanni kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito sun bayyana cewa ya yi murabus.

Alkalin Alkalai Onnoghen ya yi murabus - Shafin yanar gizo ya yi ikirari

Alkalin Alkalai Onnoghen ya yi murabus - Shafin yanar gizo ya yi ikirari
Source: Twitter

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa, dakataccen Alkalin Alkalai na Najeriya Onnoghen, a Yammacin ranar Alhamis, 4 ga watan Afrilu, ya mika wa shugaban kasa Muhammadu Buhari takardar sa ta sauka daga kujerar sa a matsayin mafi kololuwar Mai Shari'a na kasar nan.

Jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, sashe na 306 cikin kundin tsarin mulkin kasar nan ya yi tanadi na amincewa da murabus din Onnoghen cikin gaggawa. Kazalika sakin layi na daya a sashen na 292 cikin kundin tsarin mulkin kasa, ya yiwa shugaban kasa lamunin tursasa Alkalin Alkalai ya yi murabus gabanin cikar shekarun sa na ajiye aiki.

KARANTA KUMA: Rashin kulawar gwamnati ya sanya ake yiwa Mata Fyade da cin zarafi a jihar Ekiti - Erelu Fayemi

Cibiyar NJC a ranar Laraba 3 ga watan Afrilu, ta yanke shawarar tursasa ajiyar aiki ta Alkalin Alkalai Onnoghen biyo bayan takaddamar zargin sa da hukumar hana yiwa tattalin arzikin kasa ta'annati ta EFCC ta yi.

Mambobin cibiyar da suka halarcin wannan zama da sanadin jagorancin Umaru Abdullahi, tsohon shugaban kotun daukaka kara, sun amince da cewar Onnoghen ya rasa duk wata cancanta ta ci gaba da kasancewa Alkalin Alkalai na kasa sakamakon zargin da ke kansa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel