Rashin kulawar gwamnati ya sanya ake yiwa Mata Fyade da cin zarafi a jihar Ekiti - Erelu Fayemi

Rashin kulawar gwamnati ya sanya ake yiwa Mata Fyade da cin zarafi a jihar Ekiti - Erelu Fayemi

Uwargidan gwamnan jihar Ekiti, Erelu Bisi Fayemi, ta yi kira na neman dukkanin masu ruwa da tsaki da su mike tsaye wurjanjan wajen hadin gwiwa tare da gwamnatin jihar domin yakar ta'adar fyade da keta haddin Mata.

Mai dakin Gwamna Kayode Fayemi, ta bayyana damuwar ta matuka kan yadda mummunar ta'ada ta fyade, cin zarafi da kuma keta haddin mata ke ci gaba da kasancewa annoba da kuma sarkakiya a tsakankanin al'umma.

Bisi Erelu Fayemi

Bisi Erelu Fayemi
Source: UGC

Bisi ta ce duk da irin shimfidar dokoki da gwamnati ta gindaya masu haramci a kan cin zarafi, ana ci gaba da samun aukuwar munanan ababe na fyade, keta haddi da kuma cinikayyar Mutane a kulli Yaumin cikin jihar.

Ta alakanta aukuwar ababen na fasadi a ban kasa da irin rikon sakainar kashi da kuma mummunar rawar da gwamnatin baya ta taka wajen riko da akalar jagoranci a sanadiyar rashin tsaurara matakai da nagartattun dokoki.

KARANTA KUMA: Ku yiwa 'ya'ya Mata kyakkyawar tarbiya - Imamu Bako

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, Bisi ta bayyana a ranar Alhamis yayin taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a kan yakar cin zarafi da keta haddi, inda ta ce gwamnatin baya ta bar baya da kura da a yanzu gwamna mai ci zai sha fama wajen magance wannan annoba.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel