A fara laluben watan Sha'aban a ranar Juma'a - Sarkin Musulmi

A fara laluben watan Sha'aban a ranar Juma'a - Sarkin Musulmi

- Sarkin Musulmi Alhaji Abubakar Sa'ad, ya nemi al'ummar Najeriya da su sanya idanun lura wajen duban jaririn watan Sha'aban

- Watan Sha'aban shi ne wata na takwas a shekarar Musulci

- Watan Ramadan shi ne wata na 9 da ke biyo bayan watan Sha'aban

Sultan na Sakkwato, Alhaji Abubakar Sa'ad, ya yi kira na neman Musulmai al'ummar Najeriya, da su sanya idanun lura wajen duban sabon jaririn watan Sha'aban na shekarar 1440 bayan Hijirar Mafificin Halitta daga birnin Makka zuwa Madinah.

A fara laluben watan Sha'aban a ranar Juma'a - Sarkin Musulmi
A fara laluben watan Sha'aban a ranar Juma'a - Sarkin Musulmi
Source: UGC

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, Sarkin Musulmi ya yi wannan kira ne a ranar Alhamis, 4 ga watan Afrilu cikin wata sanarwa da sa hannun jagoran kwamitin fadar sa a kan harkokin da suka shafi addini, Farfesa Sambo Junaidu.

Farfesa Junaidu ya yi shellar fara duban jaririn watan a gobe yayin da ta kasance ranar Juma'a, 5 ga watan Afrilu, da za ta yi daidai da ranar 29 ga watan Rajab na Kalandar Musulunci a shekarar 1440.

A cewar sa, ana neman al'ummar Musulmi na Najeriya da su sanya na Mujiya wajen duban sabon watan a ranar Juma'a tare da gaggauta shigar da rahoton ganin sa zuwa ga Dagaci ko kuma Mai Unguwa na kurkusa.

KARANTA KUMA: Harin 'yan bindiga sun salwantar da rayuwar mutum 1, Mutane 3 sun jikkata a Bokkos

Yayin da watan Azumin Ramalana ke biyo bayan watan Sha'aban, Sultan na Sakkwato ya yi addu'a ta rokon Mai Duka ya jibinci lamari tare da shige gaban dukkanin Musulmi wajen sauke nauyin Bauta da rataya a wuyan su kasancewar su Bayi a gare sa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel