Yanzu-yanzu: An kori dan sanda mai mukamin sufeta saboda kisar Kolade Johnson

Yanzu-yanzu: An kori dan sanda mai mukamin sufeta saboda kisar Kolade Johnson

Mun samu labari daga Channels tv cewa Rundunar 'yan sandan Najeriya ta kori wani jami'inta mai mukamin sufeta daga aiki saboda harbe wani matashi Kolade Johnson har lahira.

Kakakin rundunar 'yan sanda na jihar Legas, Mr Bala Elkana ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis.

Yanzu-yanzu: An kori dan sanda mai mukamin sufeta saboda kisar Kolade Johnson

Yanzu-yanzu: An kori dan sanda mai mukamin sufeta saboda kisar Kolade Johnson
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Yadda PDP ke kokarin hana Lawan zama shugaban majalisar dattawa - Majiyar APC

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta gudanar da bincike a kan jami'anta biyu da ke aiki da sashin yan sanda masu yaki da fashi da makami (SARS) da ake zargi da kashe wani matashi Kolade Johnson a Legas a ranar 1 ga watan Maris.

An sallami dan sanda daya daga aiki bayan an tabbatar da rashin bin dokan aiki a yayin harbin da ya yi wadda ya yi sanadiyar rasuwar matashin.

Legit.ng ta gano cewa an mika 'yan sandan zuwa sashin binciken mayan laifuka CID da ke Panti a jihar Legas.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel