Ba kudin cin hanci ba ne, kyauta ce aka bani lokacin bikin diya ta - Onnoghen

Ba kudin cin hanci ba ne, kyauta ce aka bani lokacin bikin diya ta - Onnoghen

- Alkalin alkalan Najeriya da aka dakatar, Walter Onnoghen ya kare kansa daga sabbin kararakin da EFCC ta shigar a kansa

- A karar da ta shigar, Hukumar EFCC tayi ikirarin cewa kudaden da aka samu a asusun ajiyar Walter Onnoghen na cin hanci ne

- Da ya ke kare kansa, Onnoghen ya ce kudaden gudunmawa ne aka bashi a lokacin da diyarsa za tayi aure a 2015

Justice Walter Onnoghen, Alkalin alkalan Najeriya da aka dakatar ya ce wasu daga cikin kudaden da aka tura cikin asusun ajiyarsa na banki a shekarar 2015 gudunmawan bikin auren diyarsa ne ba toshiyar baki bane kamar yadda hukumar yaki da masu yiwa arzikin kasa zagon kasa EFCC tayi ikirari.

Ba kudin cin hanci ba ne, kyauta ce aka bani lokacin bikin diya ta - Onnoghen

Ba kudin cin hanci ba ne, kyauta ce aka bani lokacin bikin diya ta - Onnoghen
Source: Twitter

A cikin karar da ta shigar a gaban Majalisar Koli ta bangaren shari'a, NJC a zaman da tayi a ranar Laraba, EFCC tayi ikirarin cewa an tura wa Onnoghen wasu kudade a cikin asusun ajiyarsa a 2015 da suka ce toshiyar baki ne bisa wasu shari'a da ake yi a kotun koli a lokacin Onnoghen na shugaban kotun.

DUBA WANNAN: Jerin sunayen sojojin Najeriya da ISWA ta hallaka

Sai dai a wasikar da lauya mai kare wanda ake zargi ya aikewa R.A. Lawal-Rabana, SAN; Okon Nkanu Efut, SAN; J.U.K. Igwe, SAN; George Ibrahim, Esq; Victoria Agi, Esq; Orji Ude Ekumankama, Esq; Opeyemi Origunloye, Esq; Temitayo Fiki, Esq da lauyan da ke jagorantar tawagar EFCC, Rotimi Oyedepo, Onnoghen ya musanta zargin da akayi a kansa inda ya ce kudin gudunmawar aure ne kamar yadda aka saba yi a al'adansu.

"Kotu za ta iya ganin cewa kyaututukan kudi N250,000, N350,000, N250,000, N300,000 and N100,000 da aka bawa Onnoghen an aike da su ne lokacin bikin diyarsa. Hujjojin da aka gabatar sun nuna cewa ba sake tura wasu kudaden ba kafin bikin da kuma bayan bikin."

Lauya mai kare Onnoghen ya cigaba da cewa wannan ba laifi bane kamar yadda sashi na 13.5(2) ya dokar aikin alkalai na 2006 ya nuna saboda haka al'adan mutanen su yake kuma kudaden ba su da wata alaka da aikinsa a matsayin alkali.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel