Kotu ta bukaci Saraki, Dino Melaye, da Ben Bruce, su amsa kiran da hukumar 'yan sanda ta ke yi musu

Kotu ta bukaci Saraki, Dino Melaye, da Ben Bruce, su amsa kiran da hukumar 'yan sanda ta ke yi musu

A shekarar da ta gabata ne Bukola Saraki, Dino Melaye, Ben Bruce da kuma wasu daga cikin jiga-jigan jam'iyyar PDP suka gabatar da zanga-zanga a cikin birnin Abuja, inda suka bukaci hukumar zabe ta gabatar da zabe ba tare da magudi ba

Kotun koli ta tarayya ta bukaci Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, Sanata Ben Bruce da kuma Dino Melaye da su amsa kiran da hukumar 'yan sandan ta ke yi musu, wanda ke da alaka da zanga-zangar da suka gabatar a ranar 5 ga watan Oktoba 2018, wanda suka gabatar tare da 'yan jam'iyyar PDP.

Mai shari'a Okon Abang shi ne ya bayyana hakan a yau Alhamis dinnan, a lokacin da ya ke gabatar da karar da suka kawo mishi akan bukatar abi musu hakkinsu.

Kotu ta bukaci Saraki, Dino Melaye, da Ben Bruce, su amsa kiran da hukumar 'yan sanda ta ke yi musu
Kotu ta bukaci Saraki, Dino Melaye, da Ben Bruce, su amsa kiran da hukumar 'yan sanda ta ke yi musu
Source: Facebook

Alkalin ya ce, duk da dai ba wai ana tuhumar su bane, ya kamata ace sun kai kansu ga hukumar 'yan sanda, tun da har ta bukaci ganin su. Ya bayyana cewa kotu ba ta da ikon da zata hana hukumar 'yan sanda aikin su mutukar suna yin shi akan yadda doka ta tanada.

Sanatocin sun bukaci kotu ta bi musu hakkin su akan takardar da su ka samu ranar 6 ga watan Oktoba 2018, da hukumar 'yan sanda ta bukaci su bayyana a gabanta. Sun bayyana cewa takardar da hukumar 'yan sandan ta aiko musu, hanya ce ta son a ci mutuncin su kuma a tona musu asiri.

KU KARANTA: An kashe wata 'yar Najeriya da aka kama tana safarar kwayoyi a Saudiyya

Sannan Sanatocin sun bukaci kotu ta bi hakkinsu akan saka musu barkonan tsohuwa da aka yi wanda suka ce ya sabawa dokar kasa, sannan sun bukaci kotu ta saka a biyasu naira miliyan dari biyar, a matsayin fansa na bata musu suna da aka yi. Sanatocin uku suna daga cikin 'yan jam'iyyar PDP da suka gabatar da zanga-zanga a ranar 5 ga watan Oktoba 2018.

Hukumar 'yan sanda ta bayyana cewa Sanatocin da wasu jiga-jigan jam'iyyar PDP sun gabatar da zanga-zanga, inda su ka rufe hanyar Shehu Shagari, dalilin da ya sa suka hana mutane zirga-zirgar su ta yau da kullum. Sannan sun yi kokarin shiga helkwatar 'yan sanda ta karfin tsiya. 'Yan sandan sunyi kokarin hana su shiga helkwatar suka ki, inda su ka yi amfani da barkonan tsohuwa su ka dakatar da su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Online view pixel