Za a gabatar da shari'ar wanda ya kashe musulmai a New Zealand gobe

Za a gabatar da shari'ar wanda ya kashe musulmai a New Zealand gobe

- A gobe ne za a fara sauraron karar wannan baturen da ya kashe musulmai 50 a kasar New Zealand

- Mutumin ya bukaci kotu ta barshi ya wakilci kanshi a goben

Kotu tana tuhumar mutumin nan da ya kai hari garin Christchurch dake kasar New Zealand, wanda ya kashe musulmai lokacin da su ke sallah a masallaci, da laifin kashe mutane 50, sannan kuma ta na tuhumar shi da kokarin kashe mutane 39.

Baturen mai suna Brenton Harrison Tarrant, mai shekaru 28 a duniya, kotu na tuhumar shi da kashe mutane 50 a masallacin Al Noor da kuma masallacin Linwood, wanda ya dauki bidiyon lokacin da ya ke harbin na su ya saka a shafinsa na Facebook a ranar 15 ga watan Maris.

Za a gabatar da shari'ar wanda ya kashe musulmai a New Zealand gobe

Za a gabatar da shari'ar wanda ya kashe musulmai a New Zealand gobe
Source: Twitter

Za a saurari karar Tarrant a gobe Juma'a 5 ga watan Afrilu, a babbar kotun Christchurch. Za a nuna shi a bidiyo a lokacin da ake gabatar da shari'ar ta shi a kotu.

Alkalin da zai saurari karar ya ce za a saurari karar ne akan Tarrant zai wakilci kanshi a kotun. Tarrant ya ce shi ne zai wakilci kanshi.

KU KARANTA: 'Tun ina 'yar shekara 8 mahaifina ke kwanciya da ni'

A watan Maris din da ya gabata ne aka kama Tarrant da laifin harbe musulmai guda 50 a masallacin Al Noor da kuma masallacin Linwood da suke garin Christchurch a kasar New Zealand.

Tarrant ya kaiwa musulman hari a dai dai lokacin da suke sallah a masallaci, inda ya yi amfani da wayarshi ya dauki bidiyo lokacin da yake harbin na su, bayan ya gama ya saka a shafinsa na Facebook.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel