Babban dalilin da yasa talauci yayi ma Arewa katutu – daga bakin Dangote

Babban dalilin da yasa talauci yayi ma Arewa katutu – daga bakin Dangote

Shahararren dan Najeriyan nan da yayi fice a duniya a bangaren kasuwanci, kuma bakar fata da yafi arziki a Duniya, Alhaji Aliko Dangote ya bayyana babban dalilin da yasa bakin talauci yayi ma yankin Arewacin Najeriya katutu.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Dangote ya bayyana haka ne a yayin da yake jawabi a taron zuba hannun jari na jahar Kaduna daya gudana a ranar Laraba, 3 ga watan Afrilu, inda yace dole talauci ya cigaba da rarakar Arewa duk da arzikin noman da suke dashi, matukar basa habbaka harkar noman.

KU KARANTA: Kalli wasu alherai da babban Alkalin Alkalan Najeriya zai samu idan yayi murabus cikin ruwan sanyi

Babban dalilin da yasa talauci yayi ma Arewa katutu – daga bakin Dangote
Dangote a taron
Source: UGC

Attajirin ya kara da cewa Arewa zata iya samun arzikin da yafi arzikin mai daga harkar noma, amma fa sai sun dage wajen ingantawa tare da habbaka noman, kuma hakan zai yiwu ne kadai ta wajen hada kai da kamfanoni masu zaman kansu.

“Arewacin Najeriya zata cigaba da ci baya idan har jahohi basu rage tazarar dake tsakaninsu da takwarorinsu na sauran yankunan kasar ba, don haka yasa muke addu’ar Allah Yasa mu samu gwamnoni kamarsu El-Rufai guda 10.

“Abin damuwa ne ace Arewa dake da kashi 57 na jama’an Najeriya, da kuma kashi 70 na kasa a Najeriya, amma kashi 21 ta iya samarwa na kudaden shiga a Najeriya a shekarar 2017, don haka ya kamata Arewa ta dage wajen habbaka noma, bai kamata da wannan arzikin amma ace talauci ya damemu ba.” Inji shi.

Daga karshe Attajirin yace “Muna da damar da zamu sauya akalar tattalin arzikin Najeriya, kuma ina fata duka gwamnoni 19 zasu farka daga baccin da suke yi, kuma su yi koyi da gwamnatin jahar Kaduna.”

Dangote ya tabbatar ma mahalarta taron cewa a yanzu haka daga jahar Kano sai jahar Kaduna wajen tara kudaden shiga mafi yawa a tsakanin jahohin Arewacin Najeriya guda goma sha tara.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel