Laifin kisan Miji: Babbar kotun tarayya tayi watsi da bukatar Maryam Sanda

Laifin kisan Miji: Babbar kotun tarayya tayi watsi da bukatar Maryam Sanda

Wata babbar kotu dake zamanta a unguwar Maitama cikin garin Abuja ta yi watsi da bukatar da Maryam Sanda ta mika a gabanta na cewa bata da magana a karar da aka shigar da ita gaban kotun kan tuhumarta da ake yi da kisan mijinta Bilyaminu Bello.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito bukatar da Maryam Sanda ta mika ma kotu na nufin lauyan dake kararta bashi da wasu gamsassun hujjoji na dangantata da laifin da ake tuhumarta da aikatawa, don haka ta nemi kotu ta yi watsi da shari’ar gaba daya.

KU KARANTA: Kalli wasu alherai da babban Alkalin Alkalan Najeriya zai samu idan yayi murabus cikin ruwan sanyi

Laifin kisan Miji: Babbar kotun tarayya tayi watsi da bukatar Maryam Sanda

Bilyaminu da Maryam Sanda
Source: UGC

Sai dai Alkalin kotun, Yusuf Halilu ya nemi Maryam ta fara kare kanta daga tuhume tuhumen da ake yi mata saboda kwararan hujjojin da bangaren masu kara suka bayyana ma kotu, don haka ya zama wajibi ya saurari bangaren Maryam don jin nata jawabin.

A hannu guda kuma, Alkali Halilu ya sallami mahaifiyar Maryam, Maimuna Aliyu da yayanta Aliyu Sanda, da kuma yar aikinsu Sadiya Aminu, inda yace bai kamasu da laifi ko hannu cikin ta’asan da Maryam ta tafka ma mijinta ba.

Daga karshe Alkalin kotun ya sanar da ranar 6 ga watan Mayu don cigaba da sauraron karar, inda ake sa ran Maryam zata bada nata jawabin ga kotu kafin kotu ta kai ga yanke hukunci, sa’annan Alkali yace a kullum za’a dinga sauraron karar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel