Rashin tsaro: Kotun sauraron korafin zabe ta canja matsuguni daga Zamfara

Rashin tsaro: Kotun sauraron korafin zabe ta canja matsuguni daga Zamfara

Kotun sauraron korafin zaben gwamna da mambobin majalisar dokoki da aka kafa a jihar Zamfara ta tattara komatsanta ta bar Gusau, babban birnin jihar, ta koma Abuja saboda dalilan tsaro, kamar yadda kotun ta sanar.

Sakataren kotun, Barista Innocent Akidi, ne ya sanar da hakan yayin zaman farko na kotun da tayi a unguwar Wuse 'Zone 2' dake Abuja a yau, Alhamis. Ya ce akwai korafi a kalla 40 da kotun ta karba daga 'yan takara daban-daban.

Jastis Binta Fatima Zubairu ce ke jagorantar kotun, yayin da Okey I. Nwamoh da A. Y Ajanaku ke zaman mambobi.

Rashin tsaro: Kotun sauraron korafin zabe ta canja matsuguni daga Zamfara

Kotun sauraron korafin zabe
Source: Depositphotos

A zamanta na farko na ranar Alhamis a Abuja, kotun ta amince da yin wasu 'yan canje-canje a karar da aka shigar da hukumar zabe mai zaman kanta (INEC), jam'iyyar APC da Idris Mukhtar Shehu, sabon zababben gwamnan jihar Zamfara.

DUBA WANNAN: Akwai ayar tambaya a zaben jihohin Adamawa, Bauchi da Sokoto - APC

Jam'iyyar PDP da dan takararta, Muhammed Matawalle, ne suka shigar da korafi na farko a kan INEC, APC da dan takararta Idris Mukhtar Shehu, da aka zaba a matsayin gwamnan Zamfara, yayin da jam'iyyar APGA da dan takararta na gwamna a jihar, Sani Abdullahi Shinkafi, suka shigar da kara na biyu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel