Yanzu-yanzu: Buhari ya tafi Urdu (Jordan), Hotuna

Yanzu-yanzu: Buhari ya tafi Urdu (Jordan), Hotuna

Shugaba Muhammadu Buhari ya tashi daga babbar filin jirgin saman Nnamdi Azikwe dake Abuja zuwa Amma, babbar birnin kasar Urdu domin halartan taron zaman cibiyar tattalina arzikin duniya kan kasashen larabawa da Afrika ta yamma.

Mun kawo muku rahoton Shugaban kasan zai bar Abuja zuwa Amman a ranar Alhamis, 4 ga watan Afrilu domin amsa gayyatar Sarki Abdullah II bin Al-Hussein na kasar Jordan don halartan taron kungiyar tattalin arziki na duniya wanda za a gudanar a Dead Sea, Jordan.

Daga cikin wadanda suka tafi tare da shi sune gwamnan jihar Jigawa, Mohammed Badaru Abubakar; gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello; da gwamnan jihar Oyo, Ajibola Ajimobi.

Sauran sune ministan harkokin wajen Najeriya, Geofrey Onyeama; mai bada shawaran tsaro na kasa, Babagana Munguno; da sauran manyan mukrabban shugaban kasa.

Shugaba Buhari zai gabatar da wani jawabi yayin bude taron tare da Sarki Abdullahi II bin Al-Hussein da kuma babban sakataren majalisar dinkin duniya, António Guterres.

Daga nan za su hadu da sauran shugabannin tattalin arziki na duniya a wani taron da za a gudanar a cibiyar taro na Sarki Hussein Bin Talal.

Yanzu-yanzu: Buhari ya tafi Urdu (Jordan), Hotuna

Yanzu-yanzu: Buhari ya tafi Urdu (Jordan), Hotuna
Source: Facebook

KU KARANTA: Yankin Kudancin Kaduna za su bar jam'iyyar PDP

Yanzu-yanzu: Buhari ya tafi Urdu (Jordan), Hotuna

Yanzu-yanzu: Buhari ya tafi Urdu (Jordan), Hotuna
Source: Facebook

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewarku tare da mu. Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel