Balarabe Musa ya fadi abinda ya hana gwamnati dakatar da satar mutane

Balarabe Musa ya fadi abinda ya hana gwamnati dakatar da satar mutane

Wani tsohon gwamnan tsohuwar jihar Kaduna kuma jigo a kasa, Alhaji Balatabe Musa, ya ce gwamnati ta rasa dabarar siyasa wajen magance lamarin garkuwa da mutane da ya zama ruwan dare a kasar.

Ya ce miyagun mutane na tafiyarsu a kasar ba tare da sun fuskanci hukunci akan laifuffukan da suke aikatawa ba.

Tsohon gwamnan ya bayyana haka ne a ranar Alhamis, ga watan Afrilu a yayinda yake mayar da martani akan lamarin garkuwa da mutane da ya zama ruwan dare a yankin Arewacin Najeriya.

Ya bayyana cewa rashawa tare da tsananin son tara arziki cikin sauki na daga cikin dalilan da yasa miyagun ayyuka suka yi tsanani.

Balarabe Musa ya ya fadi abinda ya hana gwamnati dakatar da satar mutane

Balarabe Musa ya ya fadi abinda ya hana gwamnati dakatar da satar mutane
Source: Depositphotos

“Na farko, babu shugabanci siyasa mai tsari a kasar da zai magance matsalar. Na biyu, wassu mutane na da burin yin arziki cikin hanyar sauki a kasar.

“Kowa na neman hanyan samun kudi ba tare da yin la’akari da wace hanya ce zata kawo mishi kudin ba, wannan ya hada da shuwagabannin. Tare kuma da yanda masu laifi suke shagalin su ba tare da an hukunta su ba.

KU KARANTA KUMA: Shugabancin majalisa: Kungiyar matasan Yobe sun jadadda goyon bayansu ga Lawan

“Rundanan yan sanda zata kama mai laifi yau, washe gari za a sake shi saboda ya siya yancinsa."

Yace “Ko da an yanke musu hukuncin dauri, akwai wani abu kuma da ake kira roko. Duk wadannan ne suke kawo mana matsalolin da kasar ke fuskanta.”

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel