Shugabancin majalisa: Kungiyar matasan Yobe sun jadadda goyon bayansu ga Lawan

Shugabancin majalisa: Kungiyar matasan Yobe sun jadadda goyon bayansu ga Lawan

- Wata hadakar Kungiyar matasa sun jadadda goyon bayansu ga Sanata Lawan a matsayin shugaban majalisar dattawa

- Kungiyar ta bayyana cewa Lawan Ahmed ne yafi cancantar hawa wannan matsayi cikin dukkanin masu neman kujerar saboda kwarewarsa

- Alhaji Mustapha Bukar, jagoran kungiyar, ya bayyana matsayar kungiyan a wata hira da yayi da manema labarai a Damaturu

Wata kungiyar matasn Yobe mai suna ‘Yobe Youth Coalition For Advancement of Democracy’ (YCFAD), a ranar Alhamis, 4 ga watan Afrilu ta jadadda tsayar da Ahmed Lawan a matsayin wanda ya cancanci darewa kujerar shugaban majalisar dattawa.

Kungiyar ta kuma yi kira da sauran masu jayayya da lamarin akan su janye suma su bi.

Alhaji Mustapha Bukar, jagoran kungiyar, ya bayyana matsayar kungiyan a wata hira da yayi da manema labarai a Damaturu, babbar birnin jihar Yobe.

Shugabancin majalisa: Kungiyar matasan Yobe sun jadadda goyon bayansu ga Lawan

Shugabancin majalisa: Kungiyar matasan Yobe sun jadadda goyon bayansu ga Lawan
Source: Twitter

A cewar kungiyar, ya kamata shawarar kungiyar akan shugabancin majalisan ya zamo daya da na zababbun yan majalisa.

Kungiyar ta jadadda cewa Lawan Ahmed ne yafi cancantar hawa wannan matsayi cikin dukkanin masu neman kujerar saboda kwarewarsa.

KU KARANTA KUMA: Sabon sarkin Lafia zai shiga fada a gobe Juma'a

Sun bayyana cewa dole jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da fadar shugaban kasa su bayyana ra’ayinsu a shugabancin majalisan don kawar da duk wata masifa a majalisar.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Tags:
Online view pixel