Buhari ya gargadi jami'an tsaro a kan cin zalin 'yan Najeriya

Buhari ya gargadi jami'an tsaro a kan cin zalin 'yan Najeriya

Shugaban kasa Muhammadu ya bayyana rashin jin dadinsa a kan kisan wani matashi, Kolade Johnson, da jami'an 'yan sandan SARS suka yi a jihar Legas, tare da bayyana cewar gwamnatin tarayya ba zata yarda cin zarafin 'yan Najeriya da take hakkinsu ba.

Shugaban kasar ya yi barazanar cewar duk wanda aka kama yana aikata hakan zai fuskanci fushin hukuma.

"Gwamnati ba zata yarda da da cin zarafin 'yan Najeriya ko take hakkinsu ba. Duk jami'in tsaron da aka samu da laifin aikata hakan zai fuskanci fushin hukuma," a cewar shugaba Buhari.

A jawabin da Femi Adesina, kakakin shugaban kasa, ya fitar, shugaba Buhari ya mika sakon ta'aziyya ga iyalin matashin da aka kashe.

Buhari ya gargadi jami'an tsaro a kan cin zalin 'yan Najeriya

Buhari
Source: Twitter

Adesina ya bayyana cewar shugaba Buhari ya fuskanci cewar 'yan Najeriya sun fusata da yadda jami'an SARS ke gudanar da aikinsu, ya bayar da tabbacin cewar gwsamnati zata dauki nan bada dadewa ba.

DUBA WANNAN: Daliban kwalejin yaki ta Amurka sun ziyarci hedikwatar tsaron Najeriya

Jawabin ya kara da cewa tuni rundunar 'yan sanda ta kama tare da tsare jami'an da ake zargi da kisan matashin, sannan ya kara da cewa kwanan nan za a gurfanar da su a gaban shari'a domin a hukunta su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel