Moghalu: Mun san an tafka magudi a zaben shugaban kasa, amma ba zamu je kotu ba

Moghalu: Mun san an tafka magudi a zaben shugaban kasa, amma ba zamu je kotu ba

- Kingsley Moghalu, dan takarar shugaban kasa karkashin jamiyyar YPP, ya yi zargin cewa an yiwa jam'iyyarsa fashi da makamin kuri'un da aka kada masu

Sai dai Moghalu wanda ya yi watsi da sakamakon zaben, ya ce ba zai kalubalanci sakamakon zaben a kotu ba tunda tuni Atiku ya garzaya kotu

- Dan takarar jam'iyyar ta YPP ya ce yanzu zai mayar da hankali wajen ganin an sake fasalin tsarin zaben kasar

Kingsley Moghalu, dan takarar shugaban kasa karkashin jamiyyar YPP, ya yi zargin cewa an yiwa jam'iyyarsa fashi da makamin kuri'un da aka kada masu, inda aka karkatar da su ga wasu jam'iyyu a zaben shugaban kasa da aka gudanar ranar 23 ga watan Fabreru.

Da ya ke zantawa da The Interview, kafar watsa labarai ta yanar gizo, Moghalu ya ce yana da kwararan hujjoji da suka nuna cewa an tafka magudi a zaben.

A cewar hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, ta bayyana cewa Moghalu ya samu kuri'u 21,886 a zaben da ya gudana.

Dan takarar jam'iyyar ta YPP ya yi watsi da wannan sakamakon, sai dai ya ce ba zai kalubalanci sakamakon zaben a kotu ba.

KARANTA WANNAN: 'Idan ba zaku amince da nasarar Tambuwal ba, to ku garzaya kotu'

Moghalu: Mun san an tafka magudi a zaben shugaban kasa, amma ba zamu je kotu ba

Moghalu: Mun san an tafka magudi a zaben shugaban kasa, amma ba zamu je kotu ba
Source: UGC

Ya ce yanzu zai mayar da hankali wajen ganin an sake fasalin tsarin zaben kasar, yana mai karawa da cewa duk da bai ji dadin sakamakon zaben ba, hakan dai ya nuna matsayar 'yan Nigeria kan wanda suke so ya shugabance su.

"A matsayina na dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar YPP, a nawa ra'ayin, duk da an tafka kura kurai a zaben, amma maganar zuwa kotu bata taso ba,"a cewar Moghalu.

"Da ace mune muka zo na bayan dan takarar da ya lashe zaben, to da zamu iya garzayawa kotu. Amma ba wannan lamarin ba ne yanzu, kuma tuni wanda ya zo na biyu ya shigar da kara kotu, don haka ni yanzu zan fi mayar da hankali wajen ganin an sake fasalin tsarin zaben kasar."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel