Majalisar Dattijai tana tuhumar Buhari akan naira biliyan 90 da aka baiwa jihohin Taraba da Delta

Majalisar Dattijai tana tuhumar Buhari akan naira biliyan 90 da aka baiwa jihohin Taraba da Delta

Majalisar Dattijai ta karyata fadar Shugaban kasa akan zargin cewa kudin da aka baiwa Jihar Delta da Taraba basu da alaka da kudin da majalisar zartarwa ta tarayya ta aminta da a bayar

Majalisar ta bayyana cewa ta aminta da kudurin kamar yadda ya gabata a gabanta, rahoton da ma’aikatar kudi ta kasa ta gabatar wanda ke shafi na 402 a daftarin aiki mai taken “ Ma’aikatar kudi ta tarayyar ta mika muhimman bukatu na tilas ga Majalisar dokokin tarayya, a watan Mayu, 2018”.

KU KARANTA:A dora laifin kashe-kashen Zamfara kan Ministan Tsaro, ba a kan Gwamna Yari ba - Kungiya

Majalisar Dattijai tana tuhumar Buhari akan naira biliyan 90 da aka baiwa jihohin Taraba da Delta

Majalisar Dattijai
Source: Depositphotos

Majiyar Legit.ng ta fada cewa: Shugaban Kasa yayi da’awar cewa kudin da majalisar zartarwa ta tarayya ta aminta da cewa a bayar ga Jihohin Taraba da Delta ba shi suka yarda da shi ba. Shugaban kasar ya bayyana wannan da’awar tasa ne a cikin wasikar da ya aikewa majalisar.

Kasancewa Majalisar zartarwa ta yarda ne a kan naira biliyan saba’in da takwas da miliyan dari shida (N78.6bn) kana su kuma majalisar suka kawo naira biliyan casa’in da miliyan dari biyu (N90.2bn) a matsayin adadin kudin da suka aminta dashi.

Zance daga bakin mai baiwa Shugaban Majalisar Dattijai shawara akan kafofin yada labarai, mai suna Yusuph Olaniyonu, yace: “Majalisar za ta so tayi karin haske akan kasafin da Ma’aikatar kudi ta Kasa ta gabatar mata na nuna hakkokin Jihar Taraba ya kama naira biliyan ashirin da biyu da miliyan dari biyu kana na Jihar Delta shi kuma ya kama naira biliyan sittin da bakwai da miliyan dari tara hakan ne ya bada jimillar (N90.2bn)."

“Saboda haka, Majilisar tarayya ta amince da adadin da Ma’aikatar kudi ta kasa ta gabatar a gabanta a madadin Majalisar Zartarwa ta Tarayya domin gudanar da ayukan raya kasa. Haka kuma, Majilasar tayi batun cewa kididdigar da Ma’aikatar kudi ta kawo mata na (N78.6bn) ne don haka suke kalubalanntar Shugaban Kasa daya sanar dasu daga ina aka samu wannan adadin.

A karshe Majilasar tayi wannan bayanin ne domin kada a fadawa mutane abinda ba shikenan ba kana kuma shi ma Shugaban Kasa ya farga don suna zargin cewa makusantansa ne keda alhakin masa zagon Kasa cikin wannan wasika da aiko masu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel