Ta leko ta koma: Kotu ta cire wani sabon Sanata a kudancin Najeriya

Ta leko ta koma: Kotu ta cire wani sabon Sanata a kudancin Najeriya

- A jiya Laraba ne dai wata kotun koli ta cire wani sabon zababben Sanatan jihar Delta na jam'iyyar PDP

- An bayyana jam'iyyar PDP a matsayin wacce tta so ta yi kwange, yayin da ta bayyana shi a matsayin wanda ya ci zaben fidda gwani

A jiya Laraba ne 3 ga watan Afrilu, wata kotun koli ta cire sabon zababben Sanatan jihar Delta, Sanata Peter Nwaoboshi.

Alkalin kotun Ahmed Mohammed shi ne ya tabbatar da hakan, a lokacin da yake gabatar da shari'ar, wacce Ned Nwoko ya kawo ya ke kalubalantar Nwaoboshi a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwani wanda aka gabatar ranar 2 ga watan Oktoba a jihar Delta.

Kotun ta tabbatar da cewa Nwaoboshi, ba shine wanda ya lashe zaben fidda gwani da aka yi a jam'iyyar PDP a jihar ta Delta ba.

Ta leko ta koma: Kotu ta cire wani sabon Sanata a kudancin Najeriya

Ta leko ta koma: Kotu ta cire wani sabon Sanata a kudancin Najeriya
Source: UGC

Alkalin kotun ya bawa hukumar zabe ta kasa damar ta bayyana sunan Nwoko a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwani da kuri'u mafi rinjaye.

Sannan kotun ta hana Nwaoboshi bayyana kanshi a matsayin wanda ya lashe zaben Sanata a yankin.

Nwoko, ya kai karar hukumar zabe ta kasa, jam'iyyar PDP da kuma Nwaoboshi, domin ta dakatar da su daga bayyana Nwaoboshi a matsayin wanda ya lashe zaben Sanatan yankin, karar da lauyan shi Ahmed Raji (SAN) ya shigar, ya bukaci kotu ta aika da sunanshi zuwa ga hukumar zabe domin ta bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben.

KU KARANTA: A karo na farko Shugaba Buhari ya yi magana akan zaben Kano

Nwoko ya bayyana cewa a zaben fidda gwanin ya samu kuri'u 453 inda shi kuma Nwaoboshi ya samu kuri'u 405, sannan kuma akwai wani wanda ya fito a lokacin mai suna Paul Osaji, shi kuma ya samu kuri'u 216.

Nwoko ya ce ya yi mamaki a lokacin da yaji jam'iyyar PDP ta bayyana Nwaoboshi a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwanin.

Ya kara da cewa ya yi iya bakin kokarinshi wurin ganin jam'iyyar PDP ta bashi takararshi amma hakan ya ci tura.

A na su bangaren wadanda ake karar hukumar zabe, jam'iyyar PDP da kuma Nwaoboshi, sun bukaci kotu ta kori karar, tunda har an gama zabe ba a gama sauraron karar ba.

A karshe alkalin ya bayyana Nwoko a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwani na kujerar Sanata ta arewacin jihar Delta, wanda aka gabatar a ranar 2 ga watan Oktoba a shekaraar 2018

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel