Yankin Kudancin Kaduna za su bar jam'iyyar PDP

Yankin Kudancin Kaduna za su bar jam'iyyar PDP

- Bayan shekaru ma su tsawo da suka kwashe suna yin jam'iyyar PDP, sai gashi suna shawarar barin jam'iyyar don goyawa El-Rufai baya

- Sun ce jam'iyyar PDP ta yaudare su ba sau daya ba, sannan kuma ta mayar da su saniyar ware lokacin yakin neman zabe

Al'ummar yankin kudancin Kaduna sun fara tunanin canja sheka daga jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), wacce suka kwashe sama da shekaru 20 suna yi.

Hakan ya biyo bayan sakamakon zaben da aka gabatar a watan Fabrairu da kuma watan Maris, wanda yankin suka fito kwansu da kwarkwatarsu suka zabi Atiku Abubakar a matsayin shugaban kasa, sannan suka zabi Isa Ashiru a matsayin gwamnan jihar Kaduna.

Shawarar canja shekar ta samo asali bayan sunyi la'akari da irin koma bayan da yankin yake samu a siyasance, sannan kuma kafin a gabatar da zabe suna da tabbacin cewa 'yan jam'iyyar PDP da suke yankin arewacin Kaduna za su kawo yankin, sai kuma gashi hakan bai yiwu ba.

Yankin Kudancin Kaduna za su bar jam'iyyar PDP

Yankin Kudancin Kaduna za su bar jam'iyyar PDP
Source: Depositphotos

"Ana kiranmu wawaye da irin soyayyar da muke yi wa jam'iyyar PDP. Sannan kuma an mayar damu saniyar ware a lokacin yakin neman zabe. Mun fahimci cewar Atiku Abubakar ya turowa da yankin kudancin Kaduna kudi kimanin N1.4b, sai gashi mun tashi da naira miliyan dari."

Bacin ran 'yan PDP na kudancin Kaduna, kamar sako ne ga Isa Ashiru, da rashin cika alkawarin da ya yi na cewar za a bawa Rev. Joseph Hayab matsayin sakataren jam'iyya na jiha, da kuma Alhaji Wusono a matsayin sakataren jiha, wadanda daman sune alkawarin da muka yi da shi idan PDP ta ci mulki.

KU KARANTA: A karo na farko Shugaba Buhari ya yi magana akan zaben Kano

"Kiyayyar mu ga El-Rufa'i ita ce ta rufe mana ido muke ganin kamar Isa Ashiru ba shi da matsala, sai gashi yanzu muna dana sanin goya masa baya," in ji wani dan jam'iyyar PDP na kudancin Kaduna.

A yanzu haka dai al'ummar yankin kudancin Kadunan sun shiga rudani na siyasa, kuma suna neman mafita ido rufe don kama jam'iyyar da ta dace dasu. Al'ummar yankin sun ce zasu zauna su yi shawara akan goyawa El-Rufai baya ko kuma su cigaba da yi masa tawaye.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel