2019: Alkalin Kotu ya raba Sanata Peter Nwaoboshi da tikitin PDP

2019: Alkalin Kotu ya raba Sanata Peter Nwaoboshi da tikitin PDP

Wata Babban kotun tarayya da ke zama a Abuja ta tsige Sanata Peter Nwaoboshi daga kan kujerar da yake shirin komawa kai. Mun samu wannan labari ne daga gidan talabijin nan na Channels TV.

Alkali Ahmad Muhammad na kotun tarayya, shi ne ya yanke wannan hukunci bayan ya rusa zaben fitar da gwani da jam’iyyar PDP tayi a cikin Oktoban bara. Mai shari’a yake cewa sam ba Peter Nwaoboshi ne ya lashe zaben PDP ba.

Kotun ta nemi hukumar zabe na INEC ta bayyana sunan Ned Nwoko a matsayin ainihin ‘dan takarar PDP da ya lashe zaben 2019. Alkali Ahmad Muhammad ya ja-kunnen Peter Nwaoboshi da ya daina yawo da sunan shi ne ya ci zabe.

Ahmad Raji wanda shi ne babban Lauyan da ke kare Ned Nwoko ya maka hukumar INEC da kuma PDP a gaban kotu inda yake cewa Mista Nwoko ne ya lashe zaben fitar da ‘dan takarar Sanatan yankin Delta ta Arewa da aka gudanar a baya.

KU KARANTA: Babu wanda ya tafi Kotun karar zabe a Jihar Jigawa a 2019

2019: Alkalin Kotu ya raba Peter Nwaoboshi da tikitin PDP

Kotu tace ba Peter Nwaoboshi bane 'Dan takarar PDP a zaben 2019
Source: UGC

Raji ya kuma nemi PDP ta aikawa hukumar INEC mai zaman kan-ta sunan Ned Nwoko da bayanin cewa shi ne wanda ya lashe zaben tsaida ‘dan takara a maimakon Peter Nwoboshi wanda ya zo na biyu a zaben da aka yi da kuri’u kusan 50.

‘Dan takarar yace shi ya zo na farko a zaben bada tuta na PDP inda ya tashi da kuri’a 453, sannan kuma shi Peter Nwoboshi ya samu kuri’a 405. Paul Osaji ne ya zo na 3 da kuri’u 216, amma a karshe PDP tayi watsi da wannan zabe da tayi.

Lauyan da ke kare Nwaoboshi yana ganin cewa bai dace kotu ta yanke wannnan hukunci ba domin kuwa an wuce lokacin sauraron irin wadannan kara. Alkali Ahmad Muhammad dai yace takarar Nwaoboshi ba ta da inganci.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel