EFCC ta cafke zunzurutun kudi har N54m a filin jirgin sama na Maiduguri

EFCC ta cafke zunzurutun kudi har N54m a filin jirgin sama na Maiduguri

- Hukumar yaki da cin hanci da hana yiwa tattalin arziki zagon kasa ta cafke zunzurutun kudi har naira miliyan 54 a filin jirgin sama na Maiduguri

- Anyi zargin cewa mutane hudu da wasu kungiyoyi biyu masu zaman kansu na da nasaba da kudaden sannan kuma ana kan bincike a yanzu haka

- EFCC ta bayyana sunayen wadanda ake zargin a matsayin Abdullahi Yarima, Francis Bako, Saraya Umaru, James K. Yadzugwa. Kungiyan mai zaman kanta ya hada da Mercy Corps da kuma Development Exchange Centre

Hukumar yaki da cin hanci da hana yiwa tattalin arziki zagon kasa (EFCC) ta cafke zunzurutun kudi har naira miliyan 54 a filin jirgin sama na Maiduguri.

Hukumar tace mutane hudu da wasu kungiyoyi biyu masu zaman kansu na da nasaba da kudaden sannan kuma ana kan bincike a yanzu haka.

Hukumar EFCC ta bayyana sunayen wadanda ake zargin a matsayin Abdullahi Yarima, Francis Bako, Saraya Umaru, James K. Yadzugwa. Kungiyan mai zaman kanta ya hada da Mercy Corps da kuma Development Exchange Centre.

EFCC ta cafke zunzurutun kudi har N54m a filin jirgin sama na Maiduguri

EFCC ta cafke zunzurutun kudi har N54m a filin jirgin sama na Maiduguri
Source: UGC

EFCC tace ta dauki matakin ne bayan ta samu rahoto daga kwararru wanda ya bada damar cafke kudin a tashar jirgin saman.

A cewar hukumar, binciken da aka yi a asusun bankin kamfanin Mercy Corps ya nuna cewa tana da asusun bankuna 15 da BVN daban-daban.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Buhari zai tafi kasar Jordan a yau

Haka zalika binciken BVN ya nuna cewa kamfanin Development Exchange Centre na da asusun banki 40 tare da BVN daban-daban.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel